✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Sun fitar da sabuwar takardar kudi

kungiyar da take kiran kanta Jamhuriyar Neja Delta ta fitar da sabuwar takardar kudi ta fam, a yayin da ta lashi takobin kafa tata kasar…

kungiyar da take kiran kanta Jamhuriyar Neja Delta ta fitar da sabuwar takardar kudi ta fam, a yayin da ta lashi takobin kafa tata kasar daga Najeriya.
kungiyar ta tsagerun da suke yawan kai wa bututun mai hare-hare a yankin, yanzu haka sun fitar da sabuwar takardar kudi ta fam kuma sun ma fara yin mu’amala ta cinikayya tsakani su da ita kamar yadda Aminiya ta samu labari, lamarin da wasu ke gani alama ce ta nuna bijire wa zaman kasa daya kamar yadda takwarorinsu na yankin kudu maso gabas ke fafutukar kafa yankin Biyafara.
Wata kungiya da ke sa ido kan al’muran duniya kan zamantakewa, wato Daily Globe ta ruwaito cewa alamu hakan sun nuna karara saboda yawan kai hare-hare ga bututun man kamfanonin da ke aikin hakar mai a yankin da kuma sauran haddasa yamutsi tsakaninsu da jami’an tsaron Najeriya da ke aiki a yankin .
kungiyar har wayau ta lashi takobin ci gaba da tayar da kayar baya har sai sun balle daga Najeriya, sun kafa tasu kasar mai suna Jamhuriyar Neja-Delta.
Majiyar labarinmu ta ci gaba da tabbatar wa Aminiya cewa yanzu haka a yankin, kungiyoyin tsageru daban-daban suna yin Allah wadai da barnar da kungiyar ke yi, yayin da wasu kuma suka sha alwashin ci gaba da mutunta afuwar da tsohon Shugaban kasa marigayi Umaru Musa ya yi masu lokacin gwamnatinsa.
Waje daya kuma Aminiya ta tattauna da wasu ’yan Najeriya mazauna yankin kan yadda suke kallon lamarin. Wani da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce: “Ba wani abu ba ne ya haifar da haka face wanna gwamnati ta Muhammadu Buhari ba ta ba su wasu mukaman gwamnati ba kuma irin dimbin kudade da gwamnatin da ta sauka ta ba su ne yanzu ba su samu ya sanya suke wannan ta’adi amma ba su yin la’akari da halin da suke jefa ’yan Najeriya da kuma sauran al’umma, musamman na yankinsu.”