✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sultan ga malamai: Ku kiyayi rungumar abin duniya

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar koli ta Addinin Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya gargadi malamai…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar koli ta Addinin Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya gargadi malamai da shugabannin addini su guji rayuwar facaka, inda ya ce hakan ba ta nuna abin koyi mai kyau ga mabiyansu.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne ta bakin wakilinsa Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman a wajen bude gasar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 32 da ake gudanarwa a Katsina.

Sarkin Musulmi ya ce, abin bacin rai ne a rika ganin wadansu malamai da suke da dimbin mabiya suna facaka da abin duniya wajen hawa manyan motocin kasaita da kwana a kan gadaje masu ruwa.

Ya ce, akwai bukatar malamai su sani cewa suna bukatar rayuwa ta mutunci da ta dace wadda kuma za ta zamo abar koyi ga mabiyansu. Ya bayyana Musulunci da addini matsakaici da yake karfafa kare mutunci da girmama sauran jama’a inda ya ce duk Musulmin kirki suna bin koyarwarsa da kyawawan akidunsa na samar da kyakkyawar al’umma.

Wakilanmu sun tattauna da malamai daban-daban kan wannan shawara ta Sarkin Musulmi kamar haka.