✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sukar gwamnati: Yanzu aka fara – Sheikh Nuru Khalid

Sheikh Nuru Khalid, malamin adddinin Musuluncin nan da aka dakatar da shi daga limanci saboda ya “tunzura mutane kada su yi zabe” ya ce ba…

Sheikh Nuru Khalid, malamin adddinin Musuluncin nan da aka dakatar da shi daga limanci saboda ya “tunzura mutane kada su yi zabe” ya ce ba zai fasa “fadar gaskiya” ga masu mulki ba.

Malamin ya jaddada hakan ne a wata hirar bidiyo da ya yi da Aminiya.

Idan ba a manta ba, a makon jiya ne kwamitin Masallacin Rukunin Gidajen ’Yan Majalisa da ke Apo ya dakatar da malamin, daga bisani kuma ya warware rawaninsa na limanci.