‘Yan Majalisar Japan sun zabi Babban Sakataren Majalisar Ministocin kasar, Yoshihide Suga, a matsayin sabon Firaminista domin ci gaba da aiwatar da manufofin Firaminista Shinzo Abe.
Suga zai maye gurbin Firaminista Abe, wanda rashin lafiya ta sa ya ajiye mukamin shekara daya kafin cikar wa’adin mulkinsa.
Bayan an zabi Suga a matsayin shugaban jam’iyyar LDP ranar Litinin, ya ce son ci gaba da gudanar da manufofin Abe ya sa shi shiga takarar.
Suga, dan shekara 71, ya samu nasara da kuri’a 314 cikin 462 da aka kada a majalisar wakilai, inda jam’iyyarsa mai mulki ta LDP ke da rinjaye.
“Bisa la’akari da sakamakon zabe, Majalisar ta yanke shawarar Yoshihide Suga ya zama Firaminista”, inji Shugaban Majalisar Wakilai, Tadamori Oshima, bayan kirga kuri’un da aka kada.
Suga rusuna wa ‘yan majalisar a lokacin da suka bayyana masa nasararsa, amma bai yi wani bayani ba.
Ana sa ran zai bayyana sunayen ministocinsa ranar Laraba, kuma ‘yan jarida na hasashen zai maido wasu ministocin gwamnatin Abe mai murabus.