✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sufeto Janar ya bayyana gaban ’yan majalisa amma ya ki amsa tambaya

Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Ibrahim Idris jiya ya bayyana gaban kwamitin bincike na majalisar dokoki kan zargin da Sanata Isah Hamma Misau ya yi…

Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Ibrahim Idris jiya ya bayyana gaban kwamitin bincike na majalisar dokoki kan zargin da Sanata Isah Hamma Misau ya yi masa  amma kuma ya ce ba zai amsa kowace tambaya ba.
Shugaban Kwamitin, Sanata Francis Alimkhena, dan jam’iyyar APC daga jihar Edo bayan ya gabatar da ’yan kwamitin ya tambayi Sufeto Janar din ya yi karin bayani kan zarge-zargen da ake yi masa.
Amma lauyan Sufeto Janar din, Alex A. Izinyon wanda ya zauna kusa da shi ya ce ina son na bayyana kasancewa ta gaban kwamitin, sai shugaban kwamitin ya tambayi lauyan “Shin kai ne Sufeto Janar”.
A wannan lokaci sai Sufeto Janar ya ce ba zan ce uffan ba ko na amsa wata tambaya  dange da zarge-zargen da ake yi mini saboda shari’ar da ke gudana a kotu.