Hukumomin Sudan sun ce za su mika tsohon Shugaban Kasar Janar Omar al-Bashir ga Kotun Duniya (ICC) mai hukunta masu aikata manyan laifuffukan yaki.
Tsohon Shugaban Kasar yana fuskantar zarge-zargen kisan kare-dangi da laifuffukan yaki da cin zarafin dan Adam sakamakon yakin da ya barke a yankin Darfur a shekarar 2003.
An hambarar da shi daga kan mulki ne a watan Afrilun bara. Ya zama Shugaban Kasa ne bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a 1989 kuma an zarge shi da yin mulkin kama-karya.
Masu shigar da kara a Kotun ICC sun gabatar da bukatar cewa sai ya fuskanci shari’a kan kashe-kashen Darfur.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe kusan mutum dubu 300, kuma mutum miliyan 2.5 yakin ya daidaita.
A watan Disamban bara ne aka yanke wa al-Bashir hukuncin daurin shekara biyu a kurukuku kan zargin cin hanci.
Masu shigar da kara a Sudan suna tuhumarsa da kashe masu zanga-zanga a lokacin da ake neman hambarar da shi.