Kotu ta dage sauraron shari’ar tsohon Shugaban Kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir kan juyin mulkin da ya kawo shi kan mulki, zuwa ranar 11 ga watan Agusta.
Bayan lauyoyi sun yi kokafin cewa wasunsu ba su samu shiga cikin kotun ba ne a ranar Talata kotun ta dage sauraron shari’ar domin a samu babban wurin da karin lauyoyi da iyalan wadanda ake zargi su samu damar halarta.
Gwamnatin Sudan ta fara gurfanar da al-Bashir ne bayan sojoji sun hambarar da gwamnatinsa sakamakon boren da ’yan kasar suka yi na nuna kin jinin gwamnatin tasa da ta yi ta mulki tun shekarar 1989.
Al-Bashir wanda ke tsare na fuskantar shari’o’i kan zarge-zargen cin rashawa da tauye hakknin jama’a da karya dokar kasa da kuma yi wa firai minista Sadiq al-Mahdi da ya kayar da shi a zabe juyin mulki.