Tsarin PayWithSpecta ya bunkasa ciniki, ta bai wa abokan hulda damar samun bashi ta yanar gizo.
Manhajar Specta, hanya mafi sauri ta samun bashi a Najeriya wacce Bankin Sterling ya bullo da ita, ta samar da kafar magance matsalar bashi ta yanar gizo wacce ake kira PayWithSpecta.
- Sterling Bank ya bullo da tsarin tallafin karatu da aiki
- Sterling Bank ya bunkasa harkar noma a Najeriya —Awosanya
- Sterling Bank ya bullo da tsarin wutar lantarki mai nagarta
Sabon tsarin zai bai wa abokin hulda damar biyan kayayyakin da saya na tsawon lokaci, yayin da za a biya masu sayar da kayan nan take, inda yake taimaka wa masu harkokin kasuwancin samun karin ciniki.
Tsarin PayWithSpecta yana bai wa abokin hulda damar sayan kayayyaki daga shagon masu sayar da kaya da ke wani wuri ko kuma sayan kayayyaki ta shafin yanar gizonsu.
Tsarin PayWithSpecta yana kuma bai wa ’yan kasuwa damar samun bashi don gudanar da harkokin kasuwancinsu.
Abokan hulda za su iya sayen kayayyaki ba tare da kudin ruwa ba a shagunan da aka tsara ga wadanda suka zabi lokacin biya na kwana 30 zuwa kwana 90 a kasa da kasha 1.75 a wata na wata bakwai zuwa wata 12 na lokacin biyan.
Shugaban Sashen Hulda da Abokin Ciniki na Bankin Sterling, Shina Atilola, wanda ya yi furucin a wata sanarwa da bankin ya fitar kwanan nan.
Ya ce sabon tsarin zai sanya abokin hulda ya sayi kayayyaki daga wani shago da kuma shafin yanar gizo a bashi.
Atilola ya bayyana cewa abokan hulda za su iya tantance iyakar bashinsu ta manhajar PayWithSpecta kamar haka: www.paywithspecta.com.
Daga nan sai su yi amfani da iyakarsu a wannan shago kuma za su iya samun kashi 30 na iya adadinsu a matsayin tsabar kudi.
Hakan zai sanya abokin hulda ya raba kudin har zuwa watanni 12 yayin da dan kasuwan zai samu kudinsa nan take.
Ya bayyana cewa idan za a shiga, abokan hulda za su bayar da bayanansu sai kawai manhajar ta bayar da bashin cikin minti biyar sannan shafin zai samar da mallaka ga abokin hulda.
Abokin hulda zai iya yin amfani da iyakar kudinsa ta hanyar samar da alamar mallaka ga duk shagon da ke yin hadaka da bankin (ta yanar gizo ko ta shago) ya kammala sayayyarsa.
Atilola ya bayyana cewa iyakar bashin za ta kasance ta tsawon wata uku kuma za a iya sabunta ta idan ba a yi amfani da ita ba kuma ba za a caje ka ba saboda rashin yin amfani da ita.
Ya kara da cewa tsarin paywithspecta ya samar da hanyar mai sauki ta bai wa abokin hulda bashi tare da ba shi damar samun kashi talatin na bashin a matsayin tsabar kudi.
Ya kara da cewa ga harkokin kasuwanci da ke kasa baki daya da ke son fara cin moriyar wannan tsari ’yan kasuwa na bukatar su ziyarci shafin yanar gizo na PayWithSpecta don yin rajista su fara samun kudi daga masu sayan kayayyaki don hakan zai kara kudin shiga ga harkokin kasuwancinsu.
Ya shawarci abokan hulda su rika sayayyar kayayyaki ta tsarin PayWithSpecta da tsarin mallakarsu ta Specta ID, inda ya ce tsarin mallaka ta Specta ID ita ce hanya mafi dacewa da aka samar a Najeriya domin yin siyayya.