A wani bangare na zagayowar Ranar Muhalli ta Duniya ta 2021 a Najeriya, Gidauniyar Sterling One Foundation ta samo masu aikin sa-kai 125 domin tsaftacewa da kuma maido da kawa da martabar Bakin Tekun Eleko.
Masu aikin sa-kan sun fito ne daga kungiyoyi da kamfanonin Rite Foods da Sterling Bank da Nigerian Donors da Proshare da Bonnie Bio Biodegradable da kuma African Cleanup Initiative.
- Yadda rashin yarda ke shafar kasuwanci —Shugaban bankin Sterling
- Yadda tallafin karatu ke habaka fasaha da hadin kai a Sterling Bank
Gidauniyar Sterling One ta ce a karkashin shirin za yi mako 52 ana kwashe datti da gurbatattun abubuwa daga gabar tekun, wanda hakan ya zo daidai da taken ranar ta bana, wato Farfado da Tsarin Muhalli.
Bikin na wannan shekarar ya kuma zo daidai da farkon Shekara 10 da Majalisar Dinkin Duniya ta ware na Farfado da Muhalli.
Shugabar Sterling One Foundation, Misis Peju Ibekwe, ta ce gidauniyar ta yi amannar cewa ingantacciyar lafiya da harkokin kasuwanci da ma arziki ba za su samu ba sai da lafiyayyen muhalli.
Ta ce a don haka, ya zama tilas kamfanoni da kungiyoyi da gwamnatoci da ma daidaikun mutane su amsa kira wajen tabbatar da samuwar lafiyayyen muhalli da kuma bin matakan tsaftce shi akai-akai.
“Allah Ya azurta mu da abokan hadin guiwa daga kamfanoni da kungiyoyi da kuma daidaikun mutane da suka himmatu wajen kare muhalli.
“A cikin sa’a biyu masu aikin sa-kai 125 daga kawayen namu sun kwashe datti mai nauyin kilogiram 1,208 da kuma kilogiram 32.2 na robobi da za a iya sabuntawa daga Bakin Tekun Eleko.
“Sun kuma taimaka wajen samun gagarumar nasarar da aka yi a Bakin Tekun Alpha a farkon shekarar nan, lokacin da Gidauniyar ta kaddamar da aikin gayya don tsaftace bakunan teku,” a cewarsa.
A nashi bangaren, Baale na Eleko, Cif Gbadebo Fatai Labiya, ya tattaro al’ummar yankin da yake jagoranta domin shiga aikin tsaftace muhallin.
Basaraken, ya yaba wa Gidauniyar da kuma irin gudunmawar da kawayenta suka bayar, sannan ya bukaci Gwamnatin Jihar Legas da ta bayar da muhimmanci wajen rayawa da kuma bunkasa ‘Eleko Beach’ ya zama babbar cibiyar yawon bude ido.
Da yake jawabi, Alexander Akhigbe, na kungiyar African Cleanup Initiative, cewa ya yi, al’ummar Eleko za ta ci gaba da aikin tsaftace bakin tekun har zuwa karshen shekara.
Ya bayyana cewa tsarin samar da arziki daga shara da aikin ya kunsa, zai samar wa al’ummar Eleko karin hanyoyin kasuwanci da sana’o’in dogaro da kai.
A game da muhimmacin kwashe shara da raya muhalli, Babban Daraktan Recycle Point, Taiwo Adewole, ya ce, muhimman hanyoyin raya muhalli sun hada da dashen itatuwa da gyara magudanun ruwa da rage tara bola da kuma tsaftace bakin teku.
A cewarsa, Gwamnatin Jihar Legas abun buga misali ce a matsayin hukumar da ta kafa dokoki da ka’idojin kula da shara da kare tsarin muhalli.
Adewole ya yi amannar cewa duk da kalubalen da matsakaitan kamfanoni ke fuskanta, gudanar da aharkoki a tsaftataccen muhalli na iya samar da ayyukan yi ga ’yan kasa.
5 ga watan Yunin kowace shekara ce aka ware a matsayin Ranar Muhalli ta Duniya, kuma babbar kafa da Majalisar Dinkin Duniyar ke amfani da ita domin wayar da kai da kuma ba da kwarin guiwar daukar matakan kare muhalli.
A shekarar 1974 ne Majalisar ta fara gudanar da bikin Ranar, ta kuma ci gaba da amfani da ita wajen wayar da kan jama’a game da abubuwan da suka danganci muhalli kamar gurbacewar teku da dumamar yanayi da yawan al’umma da samun abinci mai dorewa da kuma keta hurumin namun daji.
Ranar Muhalli ta Duniya dandamali ne na wayar da kan jama’ar duniya da ke samun mahalarta daga kasashe akalla 143 a duk shekara.
A kowacce shekara gangamin na bayar da take da kuma dandamali, inda kamfanoni da gwamnatoci da kungiyoyi da al’ummomi da kuma mashahuran mutane ke tattaunawa, su kuma ba da shawarwari kan yadda za a raya muhalli.