An tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon dogarin Shugaban Kasa na Mulkin Soja, Janar Sani Abacha da kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore.
Sowore ya nuna wa Al-Mustapha yatsa ne a taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da jam’iyyun siyasa da ’yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ya gudana a Abuja ranar Alhamis.
- Facebook ya kaddamar da manhajar gano yaran da suka bace a Najeriya
- NAJERIYA A YAU: Shin Karin Kudin Ruwa Zai Hana Tsadar?
- Kotun Kolin Indiya ta halasta wa ’yan mata zubar da ciki
A wani bidiyo da ya karade gari musamman a kafafen sada zumunta, an ga Sowore ya fuskanci Al-Mustapha a wurin taron yana kalubalantarsa kan rawar da ya taka a lokacin mulkin Sani Abacha, cewa “Abin da kuka yi wa rayuwarmu, kai da Abacha, Allah Ya yi muku.
“Ni ina tare da gaskiya kuma a kanta nake saboda ni shugaban kungiyar dalibai ne a lokacin da kuke yi wa kasa zagon kasa,” inji Sowore, wanda shi ne mamallakin kafar yada labarai ta intanet ta Sahara Reporters.
A martaninsa, an ji Al-Mustapha na cewa, “Ba ka kai inda nake a da ba. Tsakanin zahiri da hakika abubuwa daban ne guda biyu. Har yanzu ina kan abin da nake a jiya, kuma har gobe; Ai wannan ba komai ba ne.”
Sowore ya kalubalanci Shettima a taron zaman lafiya
Gabanin cacar bakin tasu, sai da aka yi wani rikicin da Sowore, inda ya fuskanci Sanata Shettima, wanda ya wakilci dan takarar Shugaban Kasa na APC, Bola Tinubu, saboda ya zauna a sahun gaba a taron.
Masu shirya taron sun bukaci Sowore da ya koma sahu na biyu, wanda hakan ya sa ya nuna rashin amincewarsa da cewa ya cancanci zama a sahun farko kamar sauran ’yan takarar shugaban kasa.
Ya kuma ce idan har Shettima, wanda wakiltar Tinubu kawai yake yi zai iya zama a gaba, me ya sa shi dan takara ba zai iya ba?
“Matsayina daya ne da mutanen da ke zaune a gaba. Na fuskance shi (Shettima) ne cewa me ya sa yake zaune a nan, alhalin Tinubu ba ya nan.
“Da a wurin nake, ba zan tsaya tashi a ba shi wuri ba, domin Tinubu ne ya kamata ya zo nan.
“Ai ba za a iya tsayawa takarar shugabancin Najeriya daga nesa ba,” inji Sowore.
Cibiyar Zaman Lafiya ta Kasa (NPC) ce dai ta shirya taron, wanda ya samu halartar ’yan takarar shugaban kasa 18 da jam’iyyun siyasa da za su fafata a zaben 2023.
Manyan ’yan takarar da suka halarta su ne tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar (PDP), tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu, wanda abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima ya wakilata (APC); tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso (NNPP) da kuma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi (LP).