✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soke zaben Abba: ’Yan kasuwa na rufe shaguna saboda fargabar rikici

Soke nasarar Abba Kabir Yusuf da kotu ta yi a matsayin Gwamnan Jihar Kano ke da wuya, ’yan kasuwa suka fara rufe shaguna suna tafiya…

Soke nasarar Abba Kabir Yusuf da kotu ta yi a matsayin Gwamnan Jihar Kano ke da wuya, ’yan kasuwa suka fara rufe shaguna suna tafiya gida.

Aminiya ta lura cewa galibin ’yan kasuwa a kasuwannin Sabon Gari, Kantin Kwari da Singa, na ta rige-rigen rufe shaguna suna tafiya gida.

Kazalika, kawo yanzu babu wani shagali ko murna daga magoya bayan APC da yake gudana.

Hatta magoya bayan APC da Aminiya ta lura sun taru a wasu muhimman tituna da ke kusa da kotun yanzu duk sun watse, sun kama gabansu.