Rundunar Sojin Saman Najeriya ta musanta labarin cewar jirginta ya kai hari bisa kuskure a kan kauyukan Jihar Kaduna.
Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ya yi watsi da rahoton a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Gabkwet ya ce rundunar ba ta kai wani samame ba a Jigar Kaduna da kewaye a cikin awanni 24 da suka gabata.
Ya kara da cewa, ba rundunar sojin saman ce kadai take kai hari da jirage marasa matuka ba a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
“Labarin da ake yadawa cewa jirgin sojin saman Najeriya (NAF) ya kashe mutane a Kaduna karya ne.
“Har ila yau, yana da muhimmanci kafofin watsa labarai su tabbatar da sahihanci labari kafin yada shi, amma abin da aka bayyana ba gaskiya ba ne,” in ji shi.
An ruwaito cewar wani jirgin soji ya jefa bom a kan masu taron Mauludi a yankin Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
An ce lamarin ya faru ne a misalin karfe 9 na daren tanar Lahadi a yankin da ke kusa da Filin Jirgin Sama na Kaduna.