Sojoji da fararen hula sun ranta a na kare bayan mayakan kungiyar ISWAP sun kai sabon hari a Karamar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.
Mayakan sun far wa Chibok ne da misalin karfe 7 da dare, inda suka yi ta harbi kan mai tsautsayi sun kona gidaje a kuayen Kutukari mai nisan kilomita 15 daga Maiduguri, babban birnin jihar.
- MDD ta yi alkawarin taimaka wa Borno kawo karshen Boko Haram
- Al-Shabaab ta kashe sojoji 30 a sansanin AU a Somaliya
“Dandazon mayaka sun kawo wa Kautikari kazamin hari, suka fatattaki sojoji, suka yi wa ’yan banga kwanton bauna; yanzu haka muna cikin daji,” inji wani dan banga bayan harin.
An kai harin ne sa’o’i kadan bayan ziyarar farko da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya kai Jihar Borno, inda ya gana da Gwamna Babagana Zulum da tubabbun mayakan Boko Haram da kuma ’yan gudun hijirar da rikicin ya shafa, tare da alkawarin taimakawa don ganin bayan ayyukan ta’addanci.
Wata majiyar soji da ke yankin Kada, mai nisan kilomita biyu daga Kautakari, ta tabbatar cewa mayakan sun ci karfin sojojin da ke kauyen bayan musayar wuta.
Wani jami’in tsaro na Civilian JTF ya ce ganin cewa mayakan nan ISWAP sun ci karfin sojoji, sai mazauna kauyen suka cika bujensu da iska domin tsira da rayukansu.
“Yanzu haka sojoji suna kokarin kora su, amma maharan suna da yawan gaske, sai harbi suke yi ta kowace kusurwa, kowa ya tsere daji domin buya, saboda haka ba zan iya sanin yawan mutanen da abin ya ritsa ba,” in ji majiyar.