Sojoji sun sako dan fim din nan na masana’antar Nollywood, Chinwetalu Agu, wanda suka kama saboda sanya rigar kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB.
An dai kama jarumin ne a saman gadar Iweka da ke Onitsha a Jihar Anambra ranar Alhamis, inda ake zarginsa da goyon bayan haramtacciyar kungiyar.
A cikin wani bidiyo da wani jarumi a masana’antar, Emeka Ike, ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Juma’a, an ga Chinwetalu da wasu wakilai biyu daga Kungiyar Jaruman Fina-finai ta Najeriya (AGN) wadanda suka je domin karbo shi daga hannun sojojin.
Daya daga cikin wakilan dai ya ce, “Muna yi muku godiya ta musamman mambobin kungiyar AGN. Shugabanmu ya turo ni nan jiya [Alhamis] saboda matsalar da Chinwetalu ya samu da sojoji.
“Na zo nan hedkwatar shiyya ta 82 ta sojojin Najeriya da ke Enugu, yanzu ga shi muna tare da shi.
“Shugabanmu, Emeka Rollas, wannan shi ne Chinwetalu Agu, kuma lafiyarsa kalau, kuma mun daidaita su da sojojin, yanzu babu wata matsala.”
Da yake mayar da martani, Chinwetalu ya ce, “Ku ci gaba da tallafa wa masana’antar Nollywood. Ita kadai ce hanyar da muke da ita ta dogaro da kai.”
Kamun nasa dai ya yi matukar yamutsa hazo a kafafen sada zumunta na zamani.