Rundunar sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram da aka yi wa lakabi Operation lafiya dole tare da hadin gwiwar ‘yan banga sun ce, a ranar Asabar 11 ga Mayu 2019 sun tarwatsa ‘yan Boko Haram a unguwarnin Ma’allasuwa da Yaga a kauyen Munye da ke jihar Borno.
Kakakin rundunar sojojin Najeriya Kanal Sagir Musa, ya ce a lokacin da dakarun suka isa kauyen duk ‘yan Boko Haram din sun tsere, sun bar mutum 54 da suka yi garkuwa da su.
A cikin wadanda aka bari akwai ‘yan mata 29 da yara maza da mata 25 kuma duk an kubutar da su.