✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 160 a Borno da Yobe

Makama ya bayyana cewa an kashe mutane kusan 16 a kauyen Ngurokaya da ke Geidam.

Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ta sojin saman Najeriya ta kashe ‘yan ta’addan Boko Haram 160 a kauyukan Bulabulin da Degbawa da ke gabar Kogin Kumadugu da tsaunin Mandara a jihohin Borno da Yobe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an kashe ‘yan ta’addan ne a ranar Alhamis bayan da jiragen yakin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) suka lalata sansanoninsu da ke gabar kogin da tsaunuka a Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

Aminiya ta samu labarin cewa, sojojin sun kai harin farko ne a maboyar ’yan ta’addan da ke Bulabubin da ke gabar Kogin Kumadugu/Yobe da ke yankin Karamar Hukumar Geidam ta Jihar Yobe.

Kwararren mai shari kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana cewa an kafa sansanin maboyar Bulabulin a matsayin wata babbar cibiyar ayyukan Boko Haram a cikin Kogin Kumadugu/Yobe.

“A kwanan nan ’yan ta’addan sun rike wuta wajen kai hare-hare kan al’ummomin da ke iyaka da Jamhuriyar Nijar,” in ji shi.

Makama ya bayyana cewa an kashe mutane kusan 16 a kauyen Ngurokaya da ke Geidam.

Ya kara da cewa, wata na’urar bom IED, ta kuma kashe ‘yan uwan ​​wadanda suka mutu, yayin da suke gudanar da jana’izar su a kauyen.

Majiyoyin soji a Maiduguri da Damaturu, sun tabbatar da cewa jiragen yakin NAF na Super Tucano sun yi raga-raga da wasu ’yan ta’adda masu yawan gaske.

Game da yadda aka kashe ’yan ta’addan, Makama ya ce: “Hare-haren da sojojin suka kai ta sama sun yi aiki tare da hadin gwiwar sojojin kasa da ke yankin da aka kai harin.

“Hare-haren da aka kai ta sama sun yi mummunar barna a sansanonin, inda suka kashe ’yan ta’adda kusan 100,” in ji shi.

Baya ga haka, ya kara da cewa, an kuma lalata manyan motoci biyu na bindigogi da wasu gine-gine na wucin gadi guda takwas a hare-haren da aka kai a ranar Alhamis din da ta gabata.

A cewarsa, harin da sojojin suka kai ta sama sun kuma kashe wasu gungun ‘yan ta’adda 60 da kwamandojinsu a tsaunin Mandara da ke Karamar Hukumar Gwoza.

Makama ya bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne yayin da aka samu bayanai cewa suna gudanar da taro kan yadda za su kai hari a barikin sojoji a Gwoza da sauran al’ummomin kan iyaka.

Ya bayyana cewa ‘yan ta’addan su 60 da aka kashe sun yi mubaya’a ne ga fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda ne, Ali Ngulde, yayin da wadanda suka tsira suka tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu.

“An kuma kalubalanci sojojin da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukan hadin gwiwa ta kasa da sama domin murkushe ’yan ta’adda,” in ji shi.