Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ’yan ta’adda 47 ciki har da manyan kwamandojin Boko Haram yayin wata arangama a kauyen Gazuwa da ke Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.
Rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai (OPHK) tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa ta farar hula (Civilian JTF) ne suka sami galabar yayin farmakin da suka kai kan daya daga cikin sansanonin ’yan ta’addan.
- Dubun mutumin da ake zargi da hada bama-bamai ta cika a Taraba
- ’Yan sanda sun cafke bata-gari 87 a Borno
An dai kai harin ne a ranar 12 ga watan Yunin 2022.
Sansanin da ’yan ta’addan suka mayar da sunan “Gazuwa ko Markas” (Hedquarters), da a da ake kira Gabchari, Mantari da Mallum Masari, sun samu mayakan sama da 3,000 da iyalansu na bangaren Abubakar Shekau.
Wani jami’in leken asiri ya shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi cewa sojojin sun yi gumurzu da mayakan Boko Haram/ISWAP a yankin gaba daya inda suka yi ta fafatawa da su har tsawon sama da sa’o’i uku.
Majiyar ta ce sojojin sun fuskanci turjiya daga ’yan ta’addan a yayin da daruruwansu suka fito kan babura da nau’ukan makamai daban-daban tare da mayar da martani ta ko ina.
Sai dai majiyar ta ce sojojin sun fafata da su cikin gaggawa inda suka kashe 47 daga cikinsu tare da tilasta wa wasu daga cikinsu tserewa saboda luguden wutar da sojojin ke antaya musu.
A cewarsa, an kashe jami’an rundunar hadin gwiwa ta farar hula biyu a yayin arangamar.
Bugu da kari, A ranar 13 ga Yunin 2022, a ci gaba da kai farmakin da ta ke kai wa ’yan ta’addan, an yi ba-ta-kashi yadda dakarun da ke yaki daga runduna ta 21 suka yi nasarar tarwatsa tare da lalata matsugunan ’yan ta’addan.
Sojojin sun kuma lalata gidajen wucin gadi sama da 700 na da matsugunan ’yan ta’addan tare da kwato babura da makamai da dama daga hannunsu.
Majiyar ta kara bayyana cewa sojojin da ba sa ja da baya sun bi su zuwa maboyarsu tare da kama wasu ’yan ta’adda biyu da ransu.
Kamar yadda Majiyar ta zagazola ta ce sansanin na karkashin jagorancin wani babban kwamanda ne mai suna Abu Ikilima da sauran shugabanni, kwamandoji da mayakan kungiyar.