Sama da mutum 30 ne, ciki har da tsofaffi, mata da kananan yara sojojin da ke mulki a kasar Myanmar suka kashe tare da kone gawarwakinsu kurmus a Jihar Kayah mai fama da rikici a kasar.
Kungiyoyin kare hakkkin dan Adam da kafafen yada labaran yankin suka rawaito cewa sojojin sun kashe mutanen ne bisa zarginsu da kasancewa ’yan tawaye ne.
- An yi wa sojar da ta fada kogin soyayya da matashi mai yi wa kasa hidima a Kwara afuwa
- Ana samun karuwar cin zarafin mata a gidajen nishadantarwa a Saudiyya
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Karenni dai ta ce ta gano gawarwakin mutanen da yaki ya daidaita, ciki har da tsofaffi wanda sojojin da ke mulkin kasar suka hallaka a kusa da kauyen Mo So da ke kusa Hpruso a ranar Asabar.
A cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, kungiyar ta ce, “Muna Allah wadai cikin kakkausan lafazi da wannan aikin na rashin imani, wanda take hakkin bil-Adama ne karara.”
Sai dai kafafen yada labaran gwamnatin kasar sun ambato sojojin kasar na cewa sun karkashe ’yan ta’adda da dama wadanda ke dauke da makamai daga cikin jiga-jigan ’yan adawa na yankin.
Sun ce dai mutanen na cikin wasu motoci ne har guda bakwai, kuma sam ba su tsaya ba lokacin da sojojin suka umarce su da su yi haka.
Wasu hotuna da kungiyar ta wallafa sun nuna wasu gawarwaki marasa kyan gani a kan wasu konannun motoci.
Amma daya daga cikin manyan kungiyoyin ’yan tawayen kasar ta kungiyar KNDF, wacce ke adawa da juyin mulkin da aka yi a kasar a watan Fabrairu ta ce ba mambobinta aka kashe ba, fafaren hula ne masu neman mafaka.
Kasar Myanmar dai ta fada cikin rikicin siyasa tun lokacin da sojoji suka hambarar da zababbiyar gwamnatin Aung San Suu Kyi, kusan wata 11 da suka gabata, inda suka yi zargin an tafka magudi a zaben watan Nuwamban da ya ba jami’iyyarta nasara.