Akalla mayakan kungiyar ISWAP 22 ne aka kashe a daidai lokacin da dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF) ke kara kai farmaki a yankin Tafkin Chadi.
Kakakin Rundunar Sojan Najeriya, Laftanar Kanar Kamarudeen Adegoke a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce a ranar Asabar dakarun hadin gwiwa na rundunar a Mallam Fatori/Damasak da suka fito daga Najeriya da Nijar sun ci gaba da sintiri daga ranar 27 ga Afrilu, 2022 don mamayewa da kuma matsa lamba kan ’yan ta’adda a yankin.
- Rasha ta harba makami mai linzami a filin jirgin saman Ukraine
- Shirye-shiryen Sallah: Biranen Arewacin Najeriya sun fara daukar harami
Kamar yadda kakakin rundunar tsaron ya ce, nasara da dakarun na su suka samu ta ta’allaka ne da irin taimakon da mayakan sama suka bayar ne yadda suka farmaki wuraren da wadannan mayakan ISWAP suke ta sama ta yadda su kuma sojojin kasa suka samu damar fatattakar su a kusa da garin Tumbun Rago.
Ya ce, “Duk da turjiyar da ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP suka yi, sojojin kasa sun fuskanci cikas da dama tare da share hanyoyin da ake hakar ma’adinan wanda ya sa suka yi mu’amala da wasu ‘yan ta’addan na Boko Haram don su cim ma nasara.”
“Bayan gudanar da aikin, wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa an kashe akalla ’yan Boko Haram 20 aka kuma a kwace bindigogi AK 47 guda 12, Turmi 60mm 1X da manyan alburusai iri-iri. Hakazalika, an lalata motocin masu dauke da bindigu da aka boye tare da wata babbar mota makare da kayayyaki da aka tanada domin ’yan ta’addan.
“Haka nan kuma akwai wata mota kirar MRAP, wacce ’yan ta’addan suka kwace daga wani sansanin Sojojin Najeriya a baya, sojojin sun sake kwato ta a wannan hari.”
“Dakarun Sashen 1 Taskforce Wulgo (MNJTF) daga Kamaru sun ci gaba da mamaye yankunan da aka ba su tare da sintiri a yankin Chikingudu, inda aka ga ba kowa a cikin su, amma sojojin sun yi karo da wasu ’yan Boko Haram biyu da suka yi mu’amala da su. sun yi yunkurin guduwa amma dakarun da ke sa ido suka dakile, an kwato babura 2 daga hannunsu.
“A halin da ake ciki, Amphibious Taskforce Darak na sashe na 1 na ci gaba da sintiri a teku domin mamaye yankunansu.”
Rundunar ta ce ta ce hare-hare ta kasa da sama sun tilasta wa ’yan ta’addan kai da komowa sakamakon matsin lambar sojojin.