✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe mai kera wa ISWAP bom

Jiragen sojin Najeriya a yankin Tafkin Chadi sun halaka wani babban kwamandan kungiyar ta'addanci ta ISWAP, Muhammed Malik

Jiragen yakin Najeriya sun halaka wani babban kwamandan kungiyar ISWAP, Muhammed Malik, wanda ke hada wa kungiyar abubuwan fashewa.

Rundunar leken asiri ta sama da kasa ta sojojin Najeriya ta kaddamar da hare-hare kan mayakan ISWAP ne a Sabon Tumbun da ke cikin Tafkin Chadi a ranar 24 ga watan Nuwamba, inda ta halaka shi tare da kama dimbin makamai da wasu mayakan a raye.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa kafar Zagazola mai bada rahotanni kan yaki da ta’addanci cewa Muhammed Malik ya rasu ne a ranar 29 ga watan Nuwamba, sakamakon munanan raunukan da ya samu a harin.

Muhammed Malik tsohon dan Majalisar Shura na kungiyar ISWAP ne a yankin Marte, kafin ya tafi kwas kan Injiniyan Kwamfuta da Samar da Abubuwan Fashewa, a wurin kungiyar ISIS a kasar Somaliya.

Bayan dawowarsa, ya jagoranci tawagar kwararru da ke kera wa kungiyar bama-bamai da kuma ba da horo kan amfani da abubuwan fashewa wajen kai hari.

Mutuwar Malik mummunan mahangurba ne ga ISWAP da take ci gaba da rasa manyanta da sansanoninta sakamakon hare-haren da dakarun Operation Hadin Kai da Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa (MNJTF) ke kai musu babu kakkautawa.