✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram da wasu mayaka 27 a Borno

An kashe shi ne a kusa da tsaunin Mandara da ke Gwoza

Sojojin Najeriya karkashin rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai sun samu nasarar kashe wani Kwamandan Boko Haram, Alhaji Modu wanda aka fi sani da “Bem-Bem” da wasu mayaka 27 a jihar Borno.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Babban Hafsan Sojin Sama Iya Mashal Oladayo Amao, ya bukaci kwamandojin rundunar su yi tsayin daka don tabbatar da cewa sun yi amfani da karfin a kan ’yan ta’addan da ke barazana ga tsaron kasar.

An kashe Bem-Bem tare da mayakansa ne a ranar uku ga watan Agusta, sakamakon wani harin da sojojin sama suka kai a tsaunin Mandara da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Wani jami’in leken asiri, ya shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ’yan tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa wani kiyasi wurin da aka lalata ya nuna cewa harin da aka kai ta sama ya yi mummunan tasiri ga ’yan ta’addan yayin da aka kashe mayakan jihadi da dama, wasu suka samu munanan raunuka.

Majiyoyi sun ce harin ya biyo bayan sahihan rahotannin sirri da ke nuni da cewa mayakan na ISWAP na haduwa da yawa da nufin kai hare-hare.

Bem Bem, ya kasance sanannen mai safarar miyagun kwayoyi wanda ya tashi daga dan fashi da makami zuwa rikakken dan Boko Haram.

Ya taka rawa wajen gudun hijirar garin Bama a shekarar 2014, da kuma kashe daruruwan mutane kafin ya ayyana kansa na a matsayin jagora a kungiyar.

Bem-Bem wanda ke aiki a karkashin kulawar babban jagoran kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, Ali Ngoshe, yana buya ne a cikin kogo a tsaunin Mandara daga inda suke hada kai hare-hare a Najeriya da Kamaru da Jamhuriyar Nijar kafin cikar ajalinsa.