Sojojin da ke aiki da rundunar da ke aikin samar da tsaro ta Operation Safe Heaven (OPSH) a Jihar Filato sun lakada wa wani direban motar Tasi mai suna Sadik Abdullahi Karafa duka, har sai da ya ce ga garinku nan.
Rahotanni sun ce sojojin da ke zaune a kasuwar Farin Gada ne suka daki mamacin, lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa daga Mangu, gabanin lokacin fara aikin dokar hana fita a daren ranar Juma’a.
- Zan tabbatar an yi wa masu yi wa kasa hidima a Katsina rigakafin COVID-19 – Masari
- ‘Bai kamata Turanci da Lissafi su zama dole wajen samun gurbin karatu ba’
Dokar dai ta kan fara aiki ne daga karfe 10:00 na dare, amma rahotanni sun ce Sadik ya dawo wajen misalin karfe 9:20 na daren Juma’ar.
Abdullahi Karafa, yaya ga mamacin ya bayyana wa wakilin Aminiya yadda lamarin ya faru.
Ya ce, “Muna zaune a gida sai muka ji kira daga wani abokinmu cewa ga dan uwanmu can na shan duka a hannun sojojin da ke Farin Gada
“Da jin haka, sai daya daga cikin kannena mai suna Umar Abdullahi ya garzaya wajen inda ya ga sojojin na dukansa. Ko da ya ce musu dan uwansa ake duka sai suka yi banza da shi, sannan suka saka Sadik din a cikin motarsu kirar Hilux.
“Bayan dawowar Umar daga wajen, sai muka yanke shawarar cewa kashegari [Asabar] za mu je wajen da suke zama a Farin Gada tun da dai 10 ta wuce a lokacin. Ko da muka je da safen sai muka iske shi a mace.
“Daga nan ne muka dauki gawarsa zuwa ofishin ’yan sanda na Katako don sanar da su abin da ya faru.
“Kwamandan sojojin mai kula da runduna ta uku ya ziyarci gidanmu don yin ta’aziyya inda ya yi alkawarin tabbatar da an yi adalci a kai. Ba za mu bari maganar nan ta tafi a banza ba, dole a yi mana adalci,” inji Abdullahi Karafa.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar sojojin ta OPSH, Ishaku Takwa, ya yi alkawarin yin bincike kafin ya tuntubi wakilin namu.
Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton bai yi hakan ba.