✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama ’yan bindiga 5 tare da gano shanu 267 da tumaki 51 a Kudancin Kaduna

Sojojin da ke Makarantar Adana Kayan Yaki na Sojin Ruwa (Naby School of Armament Technology) da ke garin Kachiya a Kudancin Kaduna ta gabatar da…

Sojojin da ke Makarantar Adana Kayan Yaki na Sojin Ruwa (Naby School of Armament Technology) da ke garin Kachiya a Kudancin Kaduna ta gabatar da wadansu mutum biyar da ake zargi da satar shanu tare da shanu 267 da tumaki 51 da sojoji suka gano a wajensu bayan samun bayani a kansu a ranar Asabar da ta gabata.

Da suke mika mutanen ga Gwamnatin Jihar Kaduna a harabar makarantar da ke Kachiya a ranar Talata, Kwamandan Barikin, Kwamanda Tanko Yakubu Sani ya bayyana miyagun ayyuka da suka hada da satar shanu da yin garkuwa da mutane da cewa ba sababbin abubuwa ba ne a yankin, inda ya sha alwashin karfafa matakan tsaro don shawo kan haka.

“Bayan mun samu labarin ganin wadansu mutane da ba a yarda da su ba a Dakin Kujama a ranar Asabar sai jami’anmu suka kai samame kuma mun yi nasarar kama shanu 267 da mutum biyar yayin da sauran suka gudu cikin daji,” inji shi.

Kwamandan ya yi kira ga jama’ar yankunan da abin ya shafa su rika bayar da  rahoto don kai dauki cikin lokaci ga duk wani motsi ko wadansu mutane da ba su yarda da su ba.

Yayin da yake karbar dabbobin a madadin Gwamnatin Jihar Kaduna, Shugaban Karamar Hukumar Kachiya, Mista Peter Agite ya yaba wa kokarin rsojojin wajen tsabtace yankin daga ayyukan batagari.

Sannan  ya roki jama’a cewa duk wanda ya san dabbarsa ta bace ya zo tare da kwararan hujjoji don gabatarwa kafin a maida masa da kayansa.