An cafke wani basarake tare da wani dan kasar Jamhuriyyar Benin saboda zargin hada baki da kuma garkuwa da mutane.
Sojojin Birged na 13 da ke Kalaba a karkashin shirin ‘Operation Akpakwu’ a Jihar Kuros Riba ne suka kama su a wani samame da suka kai
maboyarsu da kuma fallasa
musu sauran wadanda ake
zargi.
Laifuffukan da ake zargin su da aikatawa su ne fashi da kuma sace mutane suna garkuwa da su don neman kudin fansa.
Daya daga cikin wadanda ake zargi dan kasar Benin, mai shekara 23 wanda aka kama a mahadar gidan yarin da ke garin Kalaba.
An samu wadanda ake zargin ne dauke da karamar bindiga kirar gida da wata bindiga karama.
Sauran wadanda rundunar Akpakwu ta
kama su ne, Basaraken
Gargajiya Okon Essien daga kauyen Obufa Obio ta
Masarautar Okoho Nakwa
Akani Esuk da ke Kalaba.
Sai kuma wata budurwa mai shekara 22, da wani mataka mai shekara 26, an kama
su a maboyarsu a wurare
daban-daban.
Kafin mika wadanda ake zargin, Manjo SN Ikpeme, a madadin Kwamandan Birged din, Birgediya MA Abdullahi, ya ce: “Za mu mika su ga ’yan sanda su ci gaba da yi musu bincike.”
Ya ci gaba da cewa, “Lokacin da muke binciken su, dan kasar Benin din ya tabbatar da cewa ya sha yin fashi a Kalaba ta Kudu, don haka ya amsa laifin da ake zargin sa da aikatawa.”
Ya ce ita kuwa budurwar ta tabbatar da cewa ita ke ba wadanda ake zargin labarin inda za a kai farmaki.
Kazalika, jami’in sojin ya
ce, ’ya’yan Basarake Okon
Essien, ana zargin su da garkuwa da mutane suna neman kudin fansa, shi kuma daya matashin ana zargin ya kware ne wajen yi wa mutanen unguwa sata.