✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji na hada baki da ’yan bindiga-TY Danjuma

  Tsohon Ministan Tsaro, Janar TY Danjuma mai ritaya ya zargi rundunar sojan Najeriya da taimakawa hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa al’ummomin kasar inda…

 
Tsohon Ministan Tsaro, Janar TY Danjuma mai ritaya ya zargi rundunar sojan Najeriya da taimakawa hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa al’ummomin kasar inda ya yi gargadin cewa idan harin ya ci gaba to mummunan sakamakon da zai haifar sai ya fi na kasar Somailya.
 
Danjuma wanda har ila yau shi ne tsohon shugaban rundunar sojan kasa ya ce a yanzu ba za a iya dogara da sojoji ba wajen samar da tsaron jama’a ba.
 
Ya shawarci ’yan Najeriya su tashi tsaye su kare kansu ko su fuskanci kisan kare dangi.
 
Ya yi furucin ne jiya a taron yaye daliban jami’ar jihar Taraba a Jalingo inda aka bashi digirin girmamawa kan kimiyya.