Mayakan da ake zargin ’yan kungiyar IS a Yammacin Afirka (ISWAP) ne na can suna dauki-ba-dadi da sojoji a wani sansanin sojojin da ke Kudancin Jihar Borno.
Kungiyar ta yi dirar mikiya ne a garin Damboa da misalin karfe 10:30 na safiyar Laraba dauke da muggan makamai girke a kan motocin yaki inda ta yi ta harbin kan mai uwa da wabi.
- Zan ba wa masu tada tarzoma a Najeriya mamaki — Buhari
- 2023: Limami zai tsaya takarar Gwamna a Adamawa
Lamarin ya jefa jama’a cikin fargaba yayin da mutanen gari da ’yan gudun hijira suka rika ranta a na kare domin tsira da rayukansu.
Wata majiyar tsaro da ba ta amince a ambaci sunanta ba ta ce an aika jiragen yaki domin tallaffa wa mayakan kasa wadanda ke aiki da ’yan bangar garin.
“Ina mai tabbatar maka cewa wadannan yaran (ISWAP) a halin yanzu sun kaddamar da farmaki a garin Damboa.
“An kawo jiragen sama na yaki domin dafa wa sojojin kasa; Komai na karkashin kulawarmu,” a cewar majiyar tsaron.
Garin na Damboa na da nisan kilomita 100 daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno, wanda yake tushen mayakan kungiyar ta Boko Haram.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton babu karin haske game da halin da ake ciki a garin, saboda rashin maganadisun sadarwar wayar salula a garin.