✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hafsoshi 122 sun samu karin girma zuwa matsayin Janar

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta yi wa hafsoshinta 122 karin girma zuwa mukamin Manjo-Janar da kuma Birgediya-Janar.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta yi wa hafsoshinta 122 karin girma zuwa matsayin Manjo-Janar da kuma Birgediya-Janar.

Hafsoshin sojin da suka samu karin girman sun hada da Birgediya-Janar 52 da aka daga likafarsu zuwa Manjo-Janar sai kuma Kanar-Kanar 70 da suka samu karin girma zuwa Birgediya-Janar.

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar a safiyar Juma’a ta ce hafsohin sun samu karin girma ne saboda aiki da suka yi wurjanjam domin kare kasa.

Da yake taya su murna, Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, ya ce  sabuwar amanar da aka ba su na bukatar su kara jajircewa da sadaukarwa da kuma biyayya ga Najeriya da kuma kare hadin kanta.

Daga cikin wadanda suka samu karin girma zuwa mastayin Manjo-Janar har da Birgediya-Janar AA Ayanuga na Sashen Sufuri da Kirkira na rundunar da EH Akpan na Rundunar Operation Hadin Kai da NM Jega da ke Hedikwatar Tsaro da JO Ugwuoke na Sashen Jigila na rundunar.

Sauran sun hada da PAO Okoye na Sashen Ayyuka da EF Oyinlola na Sashen Ayyuka da Shirye-shirye na Musamman da AE Edet na Makaranar Aikin Injiniya da AB Mohammed Hedikwatar Rundunar a Sashen Sanya Ido da kuma MT Usman na Rundunar Tsaron Shugaban Kasa.