Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta yi wa hafsoshinta 122 karin girma zuwa matsayin Manjo-Janar da kuma Birgediya-Janar.
Hafsoshin sojin da suka samu karin girman sun hada da Birgediya-Janar 52 da aka daga likafarsu zuwa Manjo-Janar sai kuma Kanar-Kanar 70 da suka samu karin girma zuwa Birgediya-Janar.
- Rashin kara aure ke jawo karuwanci
- IPOB: Yajin aikin ’yan Arewa ya kawo tsadar abinci a Kudu
- NAJERIYA A YAU: Shin Za A Rataye Abduljabbar?
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar a safiyar Juma’a ta ce hafsohin sun samu karin girma ne saboda aiki da suka yi wurjanjam domin kare kasa.
Da yake taya su murna, Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, ya ce sabuwar amanar da aka ba su na bukatar su kara jajircewa da sadaukarwa da kuma biyayya ga Najeriya da kuma kare hadin kanta.
Sauran sun hada da PAO Okoye na Sashen Ayyuka da EF Oyinlola na Sashen Ayyuka da Shirye-shirye na Musamman da AE Edet na Makaranar Aikin Injiniya da AB Mohammed Hedikwatar Rundunar a Sashen Sanya Ido da kuma MT Usman na Rundunar Tsaron Shugaban Kasa.