✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojin Somaliya sun kashe mayakan Al-Shabab 24

Rundunar ta dakile harin mayakan a Kudancin garin Diinsoor.

Rundunar Sojin kasar Somaliya ta ce dakarunta sun hallaka mayakan kungiyar Al-Shabab guda 24 bayan dakile wani hari da kungiyar ta kaddamar kan sansanin sojin a Kudancin garin Diinsoor.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta bayyana cewa, ’yan al-Shabab din sau uku suna yunkurin kai hari a sansanin sojin da ke lardin Bay, amma dakarunta na fatattakar su, suka kuma kashe mayakan kungiyar 24.

Dakarun gwamnati sun kuma kwace makaman da ’yan Al-Shabab din ke amfani da su wajen kai wa mutane hari bayan da aka dakile hare-haren nasu kan sansanin sojin.

Rundunar sojin ta sanar da kwace sansanin Al-Shabab da ke kauyen Orshe mai nisan kilomita 50 a Gabashin garin Dhusamareb, hedikwatar Jihar Galmudug.

Lardin na Diinsoor, wani muhimmin gari ne da ke da tazarar kilomita 100 daga garin Baidoa kuma yana kan iyaka da garin Bay inda sojin kasar ke da sansanonin kariya masu karfin gaske.