✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soja ya harbe uwa da jaririnta a kan cin hancin N200 a Neja

Tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin don daukar matakin da ya dace.

Rahotanni daga Jihar Neja na cewa wani soja ya harbe wani dan acaba da wata fasinja dauke da jaririnta a unguwar Babanna da ke Karamar Hukumar Borgu ta Jihar.

Lamarin ya faru ne da yammacin Litinin a lokacin da wadanda abin ya shafa ke dawowa gida daga kasuwar mako-mako ta Babanna.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, sojan ya harbi dan acaban ne saboda ya ki ba shi cin hancin Naira 200 da ya nema, harsashin kuma ya ratsa cikinsa ya samu matar tare da jaririnta.

Wani mazaunin garin, Sa’idu Babanna ya ce, “Daya daga cikin sojojin da aka tura garin Babanna domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a ya harbe mutum uku saboda cin hancin Naira 200. A lokacin da wadanda abin ya shafa ke shiga Babanna da safe, sojoji sun bukaci Naira 200 kuma a lokacin da suke dawowa daga Babanna zuwa Nigangi a Jamhuriyar Benin, sojojin sun sake neman karin Naira 200 daga gare su, wanda suka ce ba za su iya biya ba.

“Hakan ne ya kai ga wani soja ya bude musu wuta ya kashe mutanen uku da ke kan babur din nan take.”

Wani mazaunin yankin da ba a bayyana sunansa ba ya ce, “Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin.

“Wadanda abin ya shafa dai na dawowa gida ne daga kasuwa. Lokacin da suka zo da safe sai ga sojoji da yawa a kan iyakar Jamhuriyar Benin sun tare su suka karbi Naira 200 daga wajensu. Don haka a lokacin da suka dawo, sai waeu sojoji suka sake tsayar da su, suka sake neman Naira 200, nan take dan acaban ya ki bayarwa.

“Sai da suka fara cece-kuce sai dan acaban ya buga babur dinsa da nufin tafiya, sai wani soja ya harbe shi wanda ya sa harsashin ya ratsa cikinsa, ya samu matar da yake dauke da ita, inda nan take matar da jaririnta suka mutu.”

Ya ce an kama sojan an kai shi bataliya ta 221 da ke Kainji, a Karamar Hukumar Borgu, biyo bayan kiran da hakimin ya yi wa hukumomin soji.

Ya ce matar da jaririnta sun mutu nan take yayin da mutumin dan acaban ke karbar magani a wani asibiti a Jamhuriyar Benin.

Wata majiya ta ce, “Shiga lamarin da hakimin gundumar ya yi ne ya hana lamarin rikidewa zuwa rikici tsakanin matasa da sojoji.”

Kokarin jin martanin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ci tura.

Sai dai Shugaban Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja, Alhaji Suleiman Yarima, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce matar da jaririnta sun mutu amma direban babur din ya tsira kuma yana jinya a wani asibiti da ke Parakou a Jamhuriyar Benin.

‘’Wadanda aka kashe sun fito ne daga Jamhuriyar Benin, wadanda suka zo kasuwa a Babanna domin yin siyayya.

Ya ce tuni aka aike da gawar mata da jaririnta zuwa Jamhuriyar Benin, amma ya ce ba zai tabbatar da ko an yi jana’izarsu ba.