Rundunar Sojin Najeriya ta fara bincike kan wani soja kan zargin harbe abokan aikinsa har lahira sannan ya kashe kansa a sansanin sojoji da ke Rabbah a Jihar Sakkwato.
Kakakin rundunar, Birigediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ba a tantance hakikanin abin da ya faru ba, amma dai sojan ya harbe kansa bayan hallaka abokin aikin nasa.
Nwachukwu ya kara da cewa Babban Hafsan Runduna ta 8 (GOC) kuma Kwamandan hundunar hadin gwiwa ta Operation Northwest, Hadarin Daji, Manjo-Janar Godwin Mutkut, da wasu manyan hafsoshi sun ziyarci wajen da lamarin ya auku.
A cewarsa, GOC ya jajanta wa sojojin da suka rasa abokan aikinsu a sansanin.
“Ya bukace su da su zama masu kula da junansu kuma su ba da rahoton duk wani rikici da ke faruwa a tsakaninsu don gudun sake faruwar irin hakan.
“Ya kara musu kwarin gwiwa da su kwantar da hankalinsu tare da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
“Hukumomin Sojojin Najeriya sun damu matuka game da wannan lamari mai ban mamaki kuma sun kafa kwamitin bincike don bankado abin da ya faru.
“Ana hasashen cewa sakamakon binciken zai taimaka wajen dakile irin wannan munanan lamari a nan gaba,” in ji Nwachukwu.