✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soja da ’yan sandan bogi sun shiga hannun ’yan sanda a Kano

Asirin 'yan damfarar ya tonu bayan an kai wa 'yan sanda rahoto a Kano.

’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku da ke yin sojan-gona a matsayin soja dan sanda da kuma jami’in kwastam da suka addabi mazauna birnin Kano da kewaye.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, Abdullah Haruna Kiyawa ne, ya tabbatar wa Aminiya cewa an kama jami’an tsaron na bogi ne a lokuta daban-daban suna muzgunawa jama’a tare da damfarar jama’a.

A cewarsa “A ranar 22 ga watan Mayu, 2023 da misalin karfe 11:00 ne wata tawagar sa ido da ke sintiri ta kama wani mazaunin Filin Mushe a Kano sanye da kakin sojoji yana karbar kudi a hannun mutane.

“Kazalika a ranar 5 ga watan Mayu, 2023 da misalin karfe 21:30, an samu rahoto daga wani cewa wasu ’yan sandan bogi sun kai masa hari tare da yi masa fashin wayar hannu kirar Samsung da kudinta ya kai N60,000.”

Kakakin ya ce, tawagar ta je wurin inda aka kama mutanen biyu dauke da katin shaida na ’yan sanda na bogi da kuma lambar babur mai kafa uku da ake zargin na sata ne.

Kiyawa ya kara da cewa, an samu rahoto daga wani mazaunin unguwar Gwammaja a ranar 13 ga watan Mayu, 2023, cewa wasu gungun mutane biyar a mota kirar Golf mai lamba AKD 874 DC sun yi masa fashin buhun shinkafa 17, da sunan cewa su jami’an kwastam ne.

Bayan ’yan kwanaki suka sake tare wasu mutane, nan ma suka yi musu fashin buhun shinkafa tara.

Ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifin, wanda ya kai ga kama wani mazaunin kauyen Bankaura a Karamar Hukumar Ungogo, dauke da wata bindiga kirar gida da harsasai.

Kiyawa ya ce ana kan bincike kan lamarin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.