✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Snoop Dogg ya nemi buga waka da mawakiyar Najeriya Tems

Fitaccen mawakin Rap na duniya Snoop Dogg ya roki Tems, mawakiyar Najeriya da ta yi wa Allah ta amince su yi waka tare. There can…

Fitaccen mawakin Rap na duniya Snoop Dogg ya roki Tems, mawakiyar Najeriya da ta yi wa Allah ta amince su yi waka tare.

There can be no development without peace —Buhari

Mawakin ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, in da aka ji yana cewa ta amince da bukatarsa domin shi da iyalinsa masoya wakokinta ne.

“Tems yaushe za mu yi waka tare? Kin san ni masoyin wakokinki ne.

“Don haka yanzu lokaci ya yi da ya kamata a ji mu tare a waka daya.

“Mu yi wakar da za ta yi fice a duniya. Iyalina baki daya na cashe wa da wakokinki a gida, shi ya sa nake so mu yi wata tare.

“Ina taya ki murnar shiga sabuwar shekara,” a cewarsa.

Fitaccen mawakin dai ba’Amurke ne da ya zuwa yanzu kididdiga ta nuna ya sayar da kundin wakokinsa fiye da miliyan 23 a kasar, da kuma fiye da miliyan 35 a sauran kasashen duniya.

A hannu guda kuma mawakiyar Najeriya Tems ta fara fice a duniya ne a shekarar 2020, bayan ta yi fitowa ta musamman a wakar mawaki Wizkid mai suna Essence, kuma daga baya wani fitaccen mawakin duniyar Justin Bieber shi ma ya kara nasa baitukan a cikinta.

Wannan ya sanya ta samu shiga rukunin zakarun wakokin shekarar.

Daga nan ne kuma Tems ta yi waka da fitaccen mawakin duniya Drake mai suna Fountain.

A halin yanzu dai Tems na rukuni na uku na wadanda za su iya lashe lambobin yabo na Grammy karo na 65 da za a gudanar.