Justin Bieber ya sayar da wani bangare na hakkin mallakar wakokinsa ga kamfanin wakoki na Hipgnosis Songs Capital kan kudin dala miliyan 200.
Yanzu kamfanin ne ke da hakkin mallakar wasu daga cikin wakokin Justin na baya-bayan nan – ciki har da wakar “Baby” da “Sorry”, a cewar BBC.
- ’Yan bindiga sun harba gurneti kan mutane a Zamfara
- Na tafka kuskure a tafiyar Buhari, ba zan maimaita da Tinubu ba — Naja’atu
Wannan mataki na nufin kamfanin Hipgnosis zai rika karbar kudaden sauraren duk wata waka da aka saurara a bainar jama’a ta mawakin.
Kamfanin ke da hakkin wallafa wakokin Justin Bieber da suke faifansa mai dauke da wakoki 290.
Wannan ya hada da suka wakokinsa da mawallafinsa ya saki gabanin ranar 31 ga watan Disambar 2021.
Babban hakkin mallakar tsarin nadar wakokin mawakin shi ma na cikin wannan tsari.
Kamfanin Hipgnosis bai bayyana sharudan da aka cimma ba a kwantaragin, amma wata majiya ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa darajar kwantaragin ta kai ta dala miliyan 200.
Ana samun karuwar mawakan da ke sayar da hakkin mallakarsu ga kamfanonin kide-kide – ciki har da Justin Timberlake da Shakira, wadanda suma suka cimma yarjejeniyar kwantaragi da kamfanin Hipgnosis.