✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siyasar Najeriya ta gurbace ta rasa manufa- Tanko Yakasai

Siyasar Najeriya ta gurbace ta rasa manufa- Tanko Yakasai Daga Abbas Dalibi a Legas Alhaji Tanko Yakasai daya daga cikin dattawan Arewa ya shaida cewa,…

Siyasar Najeriya ta gurbace ta rasa manufa- Tanko Yakasai

Daga Abbas Dalibi a Legas

Alhaji Tanko Yakasai daya daga cikin dattawan Arewa ya shaida cewa, a yanzu siyasar Najeriya ta lalace ta kuma rasa manufa, ya ce ana yin siyasa ne takan jam’iyya wacce ita ce matattarar mutane masu ra’ayi iri daya wadanda keyin manufa iri guda a lokacin da suka sami gwamnati domin gyara kasa.

“Daga fara siyasa da manufa aka fara amma ‘yanzu babu manufa, jam’iyya yanzu bata da ‘ya’ya, a baya ‘ya’yan jam’iya su ne jam’iyya babu wanda zai shiga wani abu na shugabancin kasa ko mukami na zabe, ina ba wanda ‘yan jam’iyya suka amince da shi ba.”

Alhaji Tanko Yakasai ya bayanan hakan ne a sa’ilin zantawarsa da ‘yan jaridu a wajen bikin cikar sarkin Fulanin Legas Alhaji (Dakta) Muhammadu Bambado shekaru 25 bisa karagar mulki wanda ya gudana jiya Asabar a Legas.