✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siyasar almajirci

A kan dauki hoton al’umma daga yara, idan aka gan su a makarantu an san an hau hanyar neman ilimi da samun wayewa, amma idan aka…

A kan dauki hoton al’umma daga yara, idan aka gan su a makarantu an san an hau hanyar neman ilimi da samun wayewa, amma idan aka gan su suna gararamba, sukan gagari al’umma. Yayin da yara kan zama abin da suka zama ta yadda manya suka nuna musu,da farko iyaye kan taka rawar gani a rayuwar ’ya’yansu daga bisani malamai su shiga gaba wajen ba da saiti ga al’umma baki daya, musamman malaman addini.

Tabbas hakki iyaye ne a matakin farko su ciyar da tufatar da ba ’ya’yansu wajen kwana. Kafin wasu shekaru wadansu yaran kan dogara da kansu ko su samu makafa a wajen makwabta, inda ake kwana a soro ko zaure.

Daga iyaye sai mutanen gari, musamman makwabta wajen sa ido da kula da yara, na karshe wanda daga hukuma wato gwamnati babu inda za a je sai hallaka. Wadansu magabata kan nemi taimako ko shawara a wajen malamai domin darajarsu. A kwana a tashi, yaran da ake kaiwa almajirci sukan koma mabarata, ba a karatun sun dogara da sa’ar tsuntsu wajen ci da sha, yayin da aka bar karatun sai rayuwar birni ta kallon fim a gidajen kallo da canis da kwallo da rike wayoyin zamanin suka dauke gurbin allo! Basu da jari sai bola, nan suke samun shakatawa. Sannan sukan ci karo da kazuwa da kirci ga cuttutuka birjik. Ita kalmar almajiri a Larabci wato Almuhajir na nufin wadanda suka yi hijira don daukaka kalmar Allah!

Kowa ya taba ganin yara, kananan yara ba takalma a cikin tsumma ga dauda, tare da kwanuka suna bara a Arewacin kasar nan, sai su cinye ranar suna yawo da leka gidajen mutane, balle idan ka je gidan abinci, inda ake sayar da shayi, ko tsire za ka ga jira suke ka aje kwanon sai sun dirar masa, mutum ya zama kamar ungulu. Babu tabbataciyar kididdiga game da yara nawa ne suke bara, amma yaran sun wuce miliyan ashirin, daga kauyuka sun taho ci-rani birane, suna nan a warwatse da sunan neman ilimi, musamman karatun allo wanda tsari ne da aka yi karnoni ana yi, kuma aka yi watsi da tasirinsa a zamanance.

A yau akan turo yara birane don a samu saukin rayuwa, wato an mayar da tsarin kamar tsarin haihuwa! Ka haifi ’ya’ya ka tura su birni, idan sun zama mutanen kirki za su nemi iyayensu, idan suka bijire duniya ta mallake su. Su zama ’yan ga ruwa, wadansu ma su zama barayi, ’yan fashi, masu garkuwa da mutane, saboda tsabar ba a damu da rayuwarsu ba. Ana samun wadansu cikin dare a masu luwadi, a sa wa wadansu mari. Tun suna kanana sun rasa soyayya, kulawa ko shiriyar iyaye, kuma a haka za su fuskanci wulakancin kare-dangi, inda idan sun yi bara sai wanda ya ga dama zai ba su dan abin da ba ya da amfani, kwado, kanzo, kuli-kuli ko dumame, ba abin da ba su ci, kuma ba su tsoron tumbinsu ya yi bindiga. Ba su da aiki sai yankan farce, shara, tallar ruwa, hidima a gidan alaramma, garada ba su da himma! Zuwan dimokuradiyya ya ba da damar dawo da martabar almajirai a kasar nan, inda da za su hada kai su samu kamun kafar ’yan siyasa, da sun taimake juna. Gwamnatocin da suka gabata sun agaza. Amma a halin yanzu almajirai sun kara shiga wani hali na wahala, domin sai an samu a ba su, ga kasa a kanjame, me na sama ya samu da zai ba na kasa!

Masu gemu da gajeren wando sun samu shiga kuma suna son ganin bayan masu bakin rawani da masu carbi da kwano! Su kansu da kyar suka yi sa’a kofar ta bude! An mayar da bara daya da almajirci a kasar Hausa, inda ake watsa wannan harka har kasashen waje, ka je Kasa Mai tsarki ka gane wa idonka. Amma abin dubawa shi ne su kansu masallatai an mayar da su wasu wuraren neman kudi, inda limamai suka zama manajoji, ta nan suke samun nasu, har su samu tikitin Hajji da Umara a nan.

Masallatai ba su zaman kansu, balle masallata! An siyasantar da addini, ta fuskar tattalin arziki a Arewa kusan fiye da rabin mutanen sun zama mabarata, inda masu lafiya da ma’aikatan sai ka iske suna roke-roke! Duk da haramcin bara ko maula, idan ba dole ba, wanda ya tambaya yana da hakki da wanda bai tambaya ba, matsalar ita ce idan ka yi shiru za a tsinci gawa!

Wannan tsarin na almajirci ya samu daurin gindin munafuncin malamai da ha’incin mahukunta domin da malamai sun fito zahiri sun ce tsarin bara ya ci karo da tsarin Musulunci da ba haka ba, haka gwamnati za ta iya kara kasafi don kula da dauke dawainiyyar almajirai a zamanantar da almajirci ta hanyoyi da dama. Abin tambaya shi ne wai me malaman da suke da ilimi da wayewa suka yi wajen kawo karshen wannan al’ada ta mabarata da almajirci? Tun asali akwai malamai attajirai, wadanda har yau akwai irin wadannan, sannan akwai wanda abin duniya bai dame su ba, a haka nake ganin akwai malaman da za su iya tsayawa a kan gaskiya da bin duk hanyar da za a bi domin tabbatar da adalci a tsakanin mutane. A haka bai kamata a bar mabiya, sarakuna da  ’yan siyasa na yin abin da suka ga dama ba, a matsayinsu na jagororin al’umma, za su iya ba da shawara da baki, a rubuce, a rediyo da talabijin ko ma a aikace, har gobe mumbari na tasiri.

Duk da irin kudaden da ake kashewa wajen shagulgulan biki, daurin aure, bukukuwa nadin sarauta ko tura ’ya’yan ’yan siyasa kasashen waje don su samo ilimi, tabbas ba abin da ya fi muhimmanci kamar a gina al’umma a tashi tare a fadi tare.Almajirai suna da amfani idan da za a kafa kamfani, kuma su kansu almajiran da suka yi nasara za su iya kafa gidauniya don ceto ’yan uwansu da suka makale a wannan tsarin na tsangaya. Takobin almajirai addu’a, kuma Allah na karbar addu’ar almajirai!

Sai an ga alama mutum zai mutu, za a iya taimaka masa da abinci ko magani, na wani lokaci, amma don ya rayu yau da gobe wato a tabbatar da ’ya’yan talakawa na zuwa makarantu, suna samun kulla a asibitoci yadda ya kamata, halin muhallinsu, suna samun tsabtataccen ruwan sha da wutar lantarki,  ba a damu ba. Idan mutum ya mutu sai a zo jana’iza, a rika nuna an so a taimaka, amma rai ya yi halinsa! Talakawa ba zasu mutu ba, kuma almajirai ba za su kare ba har abada.

Daga Buhari Daure

Kofar Kaura, Katsina

[email protected]