✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sitiyari a hannun mahaukata? (2)

Mun soma da shimfida a makon da ya wuce game da matsalar tuki da matuka da halin hankali da rashin hankali da ake fama da…

Mun soma da shimfida a makon da ya wuce game da matsalar tuki da matuka da halin hankali da rashin hankali da ake fama da shi, inda muka kare da cewa babbar matsalar da ke gabanmu dangane da abubuwan hawa ba ta wuce abin nan da Bahaushe ke cewa kura ta gudu daga hannun gardi baki bude ba! Ma’ana makasa ne ke yawo a cikin titunan al’umma. Mafasa ke kai hari a cikin shaguna ko gidajen al’umma. Mahaukata ne ke yawo da sitiyari a hannu domin tattake duk wanda tsautsayi ya kasance zai fada kansu, a zo kuma ana cewa ai abin daga Allah ne, alhali mu ne da kanmu muke daukar wuka muke soka wa kanmu, mu koma gefe guda muna ihun mun yi abin a zo, a gani!
Me ya sa muka ce haka? A koma tun daga farkon zancen, shi wannan da aka ce yana bayar da lasisin ingancin iya tukin mota shi ne ya kara tabbatar mana da halin walankeluwar da muke ciki dangane da tuki a bisa hanyoyinmu. Shi da kansa ya san cewa mahaukatan ne ke bisa hanya, shi ya sa ya kara tabbatar da batun don a kara kula.
Su wane ne mahaukatan ke nan? Bari mu dau misalai mu gani.
•    Yawancin masu abin hawan kansu, ba su koyi tukin ba kafin su fara tukin, a nan muna magana ne kan koyon tuki irin na ka’ida, bisa doka da tsari. Duk irin yadda mutum ya samu damar mallakar abin hawa, ya gwanance kansa, amma da ka ya iya ko ya sani, bai taba zama gwani, domin tuki ba abin wasa ba ne. Ke nan idan kana neman mahaukaci, ka samu a nan, domin wanda bai da isassa kan ko mene ne, ai mahaukaci ne.
•    Yawancin matukan abubuwan hawa na kasuwanci, na bas ne ko tasi ko gwangwaro ko kiya-kiya ko daf, in ka dora masu hauka a kasar nan ba ka yi laifi ba, domin ko muraran muna ganin haka a cikin kauyuka da garuruwa da biranenmu. Wane dan bas ne ke da isassa? Ko dan tasin da ya san abin da yake yi? Ko kuma dan Keke-NAPEP da ya san cewa gwadaben da yake tafe kansa rayuka ne ba makabarta ba? Wane direban motocin gwamnati na tarayya ko jiha ko karamar hukuma zai iya cin jarabawar likitin hauka ba tare da ya tabbatar mana da botsarewarsa ba? Idan kuwa haka ne ashe nan ma hauka ya tabbata!
•    Wane matukin abin hawa ke da lasisin tukin kamar yadda doka ta tanada? b.I.O da ’yan Road Safety, su ma lafiyayyu ne? Ba a jin cewa za-mu-ce-ta-tarar-da-mu-je-mu? Ta yaya wadanda suke shan maganin hauka za a mika musu mahaukata domin su kula da su? Ai ina ganin abin kamar Ummu da Aisha ne! Saboda haka batun a tsaya neman mafita, bai taso ba, sai dai a shiga neman asibitin da za a kai su, don gyara.
•    A yau ba sai an jaddada ba, kashi 90 cikin 100 kila ma fiye, na lasisin tukin kowane irin abin hawa a cikin kasar, na bogi ne! Na karya ne! Na saye da sayarwa ne! Shi wanda ke bayarwa ya san haka. Shi mai karba ya fi kowa sanin haka. Shi kuma wanda mahaukatan suka buge za su buge ko suka ko za su karairaya ko ma suka kashe ko za su kashe, ya tabbatar da haka, ba abin da wani zai iya yi a cikin kasuwar mahaukata.
A cikin irin wannan yanayi me zai hana a kullum rana ta Allah a dinga samun matsalolin gudanar da lamurra yadda suka dace a bisa titunan kasar nan baki daya? Me zai sa rayuka ba za su baci ba? Me zai sa rayuwa ba za ta dugunzuma ba?
A cikin kasar nan ne za a ga yadda jama’a ke tsara yadda za su kai ’ya’yansu makarantu da safe, ko dai su yi sammako, tunda asuba don su kauce matsin matuka ko kuma su dauki dogon zubi, ta yadda tafiyar minti 30 su yi ta a awa daya ko fiye don a kauce wa cinkoson masu abin hawa, ba kuma wai don hanyoyi ba su da kyau ba, sai dai don wani mahaukacin ya bi hanyar da ba tasa ba, ya rufe hanya, ta yadda ba mai iya yin gaba ko baya, ba mai iya yin hagu ko dama! Nan ne za ka ga matuki na rige-rige ya samu ya kutsa, wai ko ya wuce kafin wurin ya rincabe, kan ka ce kwabo, ya kara dagula lamurra. Nan in ba a yi hankali ba, sai a yi awoyi, ba mafita daga cikin dandazon jamhuriyar mahaukata!
Don Allah mene ne wannan in ba hauka ba?
• Yi wa dabbobi hon ko oda a cikin titunan kauye, wai su kauce bisa hanya.
• Tafiya bisa titi da abin hawan da bai da isasshiyar lafiya, musamman taya ko birki.
• Cunkusa mutane da dabbobi 40 ko fiye a cikin abin hawan da bisa ka’ida bai wuce ya dauki mutane da dabbobi 20 ba.
• Tsayawa tsakiyar hanya a dauki fasinja, ba tare da nuna damuwa an yi laifi ba.
• Amfani da abin hawa a wuce wani abin hawan ta bin hannun dama a maimakon na hagu.
• Gudun famfalaki a cikin unguwa ko kauye ko gari ko birni saboda gadarar ana da abin hawa.
• Ajiye abin hawa a inda bai dace a ajiye su ba, ta yadda kan ka ce kwabo an jawo cinkoso a rayuwar al’umma.
Ire-iren wadannan hanyoyin gane mahaukata yawa gare su, hanyoyin magance su ne kila suka yi kadan, sa’annan barnar da mahaukatan ke faman yi a kullum kuma bayyananniya ce. Mace-mace! Karye-karye! Guntule- guntule! Ba kuma ranar da za a bar ganin haka sai ranar da aka warkar da mu daga cutar haukar da ke damunmu duka!