Ranar Laraba da karfe 12 na dare ake rufe Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Aminya-Trust karo na farko.
Shin ku aiko da naku labaran don shiga gasar?
Idan ba ku aiko ba, sai ku hanzarta, kuma ku yi la’akari da wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku mayar da hankali a kai, kamar yadda Abubakar Adam Ibrahim ya ba da shawara.
Abubakar dai dan jarida ne kuma kwararren marubuci, musamman a fannin rubutun gajerun labarai, sannan ya lashe kyaututtuka daban-daban na adabi a lokuta daban-daban a baya.
Ya ce duk marubucin gajeren labarin da ke son lashe gasa ko wacce iri ce, dole ne ya yi la’akari da wadannan abubuwa:
Labarin na da sassa guda uku: fuska, gangar jiki da kuma kafafu.
1. Fuskar labari
A fuskar labara na da matukar muhimmanci kasancewa ita ce mai rubutu zai fara gani sannan ya yanke shawarar ci gaba da karatu ko akasin hakan.
Saboda haka, dole mai rubutu ya tabbatar ya rubuta fuska mai matukar jan hankalin masu karatu
2. Gangar jikin labari
Gangar jiki kamar a kowanne irin nau’in labari ita ce ginshiki saboda ita ke dauke da muhimmin sakon da labarin ya ke kokarin isarwa.
A cikinta ne ake samun jayayya ko sa-in-sa tsakanin gwarzon labarin da kuma abokan hamayyarsa.
3. Kafar labari
Kafa ita ce karshen labarin. A cikinta ne za a warware duk wata takaddama tsakanin gwarzon labari da kuma abokan fafatawarsa.
Kazalika, a nan ne ya kamata duk wani sako ko darasin labarin ya fito karara.
Ko da fuska da gangar jiki sun yi kyau, idan kafa ba ta yi ba sai ka ga an samu matsala.
Me ake nema a labarun a dunkule?
- Dole ne labarin ya kasance mai ma’ana tun daga farko har karshe.
- Dole ne ya warware duk wani kulli da ya yi tun daga farko har karshe, ba tare da barin masu karatu cikin duhu ba.
- Labari ya zama mai fa’aida.
- Labari ya zama yana da nasaba da jigon da aka bayar.
- ’Yan shekaru 18 zuwa 35 ne kadai su ka cancanta shiga gasar
- Dole labarin ya kasance yana da nasaba da zamantakewar Hausawa, ban da saba al’adu da rayuwarmu ta yau.
- Labaran su kiyaye dukkan sharuddan shiga gasar.
- Dole labaran su kiyaye ka’aidojin rubutu, tsarin jimloli da ka’aidar adabin Hausa.