Assalamu alaikum; barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga misalan da’a ga Allah daga mata magabata da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin:
6. “Ba zan gode wa kowa ba sai Allah! Wannan shi ne kalaman babbar mumina kuma sarauniyar muminai wadda tauraronta ya fi na kowacce mace haske a lokacin da ayoyin suka sauka suka wanke ta daga zargin yarfe da munafukai suka yi mata. Bayan Allah Ya sanar da ita cewa Allah Ya tabbatar da gaskiyarta sai mahaifiyarta ta bukaci ta je ta yi wa Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi) godiya. Wadannan kalamai nata na nuna irin fahimtar da ta yi cewa Allah ne kadai Ya cancanta da godiyarta a wannan lokaci, domin ya tabbatar da halaccin kuma Shi Ya karrama ta da saukar da hukunce-hukunce na shari’a da za su amfani Musulunci har zuwa Ranar Kiyama. Don haka a lokacin godiyar Allah ce kadai ta cika zuciyarta da ya tsamo ta daga kangin kunci da bakin cikin da take ciki, Ya saukar da ayoyin wanke ta a lokacin da masoyinta Manzon Allah (SAW) yake bukatarta in ta yi sabo ta tuba Allah Zai gafarta mata, a nan ta fadi kalamai masu nuna tsananin takawa ga yarinya mai karancin shekaru kamarta in da ta ce koma ta fada ba zai yarda da maganarta ba tun da zuciya ta karkata don haka: “Ni dai abin fadi abin da mahaifin Annabi Yusuf (AS) ya fada, hakuri shi ne mafi dacewa, Allah ne Wanda ake neman taimako (a wurinSa) a kan abin da kuke siffantawa.”
Wannan jawabi nata da yadda take Allah Ya saukar da ayoyi don wanke ta, Ya kara daukaka darajarta da kaunarta a wurin Manzon Allah (SAW), har ya rika nuna ya fi son ta sama da kowa cikin mutane. Don haka uwargida koyaushe kika zabi Allah da ladabi dokokinSa da neman kusanci da Shi, kina kara wa kanki daraja bisa daraja ne, ko da a lokacin akwai tsananin wuya kamar yadda Uwar Muminai A’isha (Radiyallahu Anha) ta yi kwana biyu tana zubar da hawaye har ciwo ya kamata saboda kunci wannan mugun kaidi da aka yi mata, amma a karshe ta samu karin daukaka sama da wacce take da ita kafin faruwar haka. Sannan duk lokacin da kika bijire wa dokokin Allah kina yage wa kanki daraja bayan daraja har sai kin kasance wata dabbar ma ta fi ki daraja kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana: “Kuma lallai ne, hakika, Mun halitta saboda Jahannama, masu yawa daga aljannu da mutane, suna da zukata, ba su fahimta da su, kuma suna da idanu, ba su gani da su, kuma suna da kunnuwa, ba su ji da su; wadancan kamar bisashe (dabbobi) suke. A’a, su ne mafiya bacewa; Wadancan su ne gafalallu.”
- “’Yata tashi ki garwaya madarar nan da ruwa.”
“Inna ba ki ji sabuwar dokar da Sarkin Musulmi ya kafa ba?
“Wace doka ce?”
“Ya sa an yi sanarwa da babbar murya cewa kada wani ya kara garwaya madara da ruwa.
“Tashi ki kara wa madarar nan ruwa, kina wurin da Umar ba zai ganki ba!”
“Ba zan ji tsoron Allah a fili kadai ba, sannan in bijire maSa a boye.”
Wannan tausasan kalamai masu cike da tsoron Allah na hakika sun fito ne daga bakin wata tabi’a yarinya mai kananan shekaru, lokacin da ta yi wannan kalamai Sarkin Musulmi Umar dan Khattab (RA) yana jingine a katangar gidansu yana saurare a yayin da yake rangadin garin Madinah kamar yadda ya saba kowane dare. Take ya bukaci wani daga cikin ’ya’yansa ya nemi auren wannan yarinya da ja musu kunnen in ba su aure ta ba, shi zai aure ta, ta zamo uwarsu. Don haka Asim bin Umar Alkhattab ya aure ta ta haifi ’ya mai suna Fatima wacce ita ta haifi baban halifan nan Umar dan Abdul’aziz wanda ake wa lakabi da Umar na biyu.
To ’yan uwa uwayen gidaje, kun ga inda tsoron Allah da kiyaye dokokinSa ya kai waccan ’yar mai sayar da madara ta samu aure a babban gida da ya fi kowanne daraja a wannan lokaci ta kuma zama kaka ga halifan da ake kwatanta shi da babban sahabin Manzon Allah (SAW) Umar bin Alkhattab (RA). Don haka tsoron Allah ba dan bukata ba ne yau a yi, gobe a aje, ko a jingine saboda wata bukata sai ta wuce a dauka. Tsoron Allah barinsa ake dindindin a cikin zuciya, a kare shi da dukkan karfi da ya ji kada ya rage ko ya fita ya bar zuciya; wannan yarinya da a ce ta jinginar da tsoron Allah ta bi umarnin mahaifiyarta da hakan zai jawo musu kaskanci ita da mahaifiyarta. Amma da ta rike tsoron Allah kyam sai Ya haifar mata daukaka da karin matsayi a duniya da Lahira, ga shi har shekaru da yawa ana buga kyakykyawan misali da ita.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.