Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga misalai daga mata magabata da yadda suka aikatar da kowane daya daga cikin wadannan sinadaran kamala; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.
Misalan Da’a Ga Allah:
- Akwai kyawawan darussa da Uwargida za ta koyi da su wajen tsare mutunci da kamun kai daga rayuwar Nana Maryamu Mahaifiyar Annabi Isa A.S; domin ta kai makura wajen nagarta har Allah Madaukakin Sarki Ya shaideta da haka cikin LittafinSa Mai Tsarki:
“Da Maryama Diyar Imrana wadda ta tsare farjinta; sai Muka hura a cikinsa daga ruhinmu; kuma ta gasgata da Ayoyin Ubangijinta da LittattafanSa, alhali kuwa ta kasance daga masu tawali’u.” Aya ta 12; Sura ta 66. Mu tuna cewa Nana Maryam ta kasance cikakka kuma lafiyayya ce kamar kowace mace, tana da bukatu irin na ’ya mace; amma ta sadaukar da dukkan bukatunta ta mika wuya gaba daya ga Ubangijinta; wannan ya sa Allah Ya yabeta da tsare farjinta kuma shi ya sa ta shiga halin damuwa matuka da jin cewa za ta haihu domin ta san da yawa daga mutane za su zargi mutuncinta wanda ya kasance abu mafi soyuwa da tsada a gareta. Amma kalaman Ubagjinta da RahamarSa suka natsar da zuciyarta ta fuskanci jama’arta ba tare da ko da digo daya na tsoro ko shakkar abin da za su ce game da ita ba domin ra’ayinsu a kanta bai da muhimmanci; matsayinta a wajen Ubangjinta shi ne kadai mai muhimmanci.
Abin koyi daga rayuwar wannan Sarauniyar Salihan mata ga Uwargida shi ne kodayaushe, komai tsananin bukata, ta rika dubi zuwa ga ya wannan abu yake a gaban Allah Madaukakin Sarki? Abu ne da zai sa ta samu lada da karin matsayi ko abu ne da zai sa ta samu zunubi da fushin Ubangijinta Madaukakin Sarki? Uwargida ki sani duk wani abu mara kyau a gaban Allah, kuma kika aikata shi kina cikin sanin haka, to wannan ba abin da zai jawo maki sai faduwar daraja a gaban Allah da kuma a gidan miji da dukkan al’amuranki na yau da kullum. Kar a rika biye wa yayi saboda an ga wance da wance na yi ko saboda sabon yayi ya shigo gari a mance da dokokin Allah a ce sai an yi abin nan komi kazancewar abin a gaban Allah; Mu yi koyi da Nana Maryam; tana ganiyar macentakarta, tana ganin sa’o’inta suna rayuwarsu daidai da al’adarsu ta lokacin, amma wannan bai ja hankalinta ba ta yi sha’awar ita ma sai ta yi haka ba, ta maida hankalinta gaba daya ga Ubangijinta da ayyukan kara kusanci zuwa gareSa. Don haka Uwargida ki yi koyi da Nana Maryam, kodayaushe ki nemi dadin Allah sama da dadin kanki ko wasu mutane makusanta, ki nemi burge Allah sama da burge mijinki, kawaye ko shiga yayi. In kika kiyaye dokokin Allah Shi zai ba ki matsayi da darajar da kishiyar hakan ba za su baki ba.
- Misali na biyu daga rayuwar Asiya matar Fir’auna, wadda duk da gawurta da izza irin na mijinta Fir’auna ta yi masa tawaye, ta bijire wa daularsa ta yi imani da Allah da Annabi Musa Amincin Allah su kara tabbata a gare shi. Ku duba mace ce da ta rayu dukkan rayuwarta cikin daula da jin dadi maras misaltuwa; barori da bayi kodayaushe na tsagaye da ita suna mata hidima; ku dubi girman mulki irin na mijinta; ku dubi irin girman imaninta ya sa duk ta yi watsi da wannan ta zabi Ubangijinta mafi daukaka. Allah Ya tabbatar da nagarta Asiya diyar Muzahim inda Ya ce:
“Kuma Allah Ya buga wani misali domin wadanda suka yi imani matar Fir’auna lokacin da ta ce “Ya Ubangiji! Ka gina mani wani gida a wurinKa cikin Aljanna. Kuma Ka tserar da ni daga Fir’auna da aikinsa kuma Ka tserar da ni daga mutanen nan Azzalumai.” Aya ta 11; Sura ta 66.
Haka ma Hadisin Manzon Allah Ya tabbatar da cikar kamalar wadannan manyan bayin Allah biyu: Abu Musa ya ruwaito Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam yana cewa da yawa daga cikin maza sun samu cikar kamala, amma ba wadda ta samu kamala daga cikin mata face Asiya matar Fir’auna, Maryam Diyar Imrana.
Sai sati na gaba Insha Allah, Da fatan Allh Ya sa a yi Sallah lafiya kuma Allah Ya sa mu kasance cikin kulaarSa a kodayaushe, amin.