✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siffofin “Windows 10” da alakarta da “Windows 7” da “Windows 8” (2)

BBC:  Mene ne bambanci tsakanin “Windows 7” da wannan da ake fitarwa a yanzu, kuma wasu abubuwa ne sababbi da suka fito a cikin “Windows…

BBC:  Mene ne bambanci tsakanin “Windows 7” da wannan da ake fitarwa a yanzu, kuma wasu abubuwa ne sababbi da suka fito a cikin “Windows 10” da ake kaddamarwa a yau?
Baban Sadik:  Wannan babbar manhaja da ake kaddamarwa a yau tana da dabi’u wadanda suka sha bamban ko suka sa ta sha bamban da sauran manhajoji da kamfanin  ya fitar a baya, kusan 13 ko sama da haka.  Amma shahararru daga cikinsu sun hada da: kayatar da tsarin mu’amala da manhajoji mai suna “Start Button” wanda tun daga nau’in Windows na zamunnan baya har zuwa kan “Windows 7” yana nan.  Idan ka shiga fuskar kwamfutarka wato “Desktop” daga bangaren hagu a kasa, akwai wata alama da idan ka matsa, za ka ga dukkan manhajojin da ke kwamfutar, a bangare daya kuma ga shafin fuskar kwamfutar kana gani.  Amma a “Windows 8” sun canza wannan tsari; da zarar ka matsa wannan alama sai ta mamaye dukkan shafin fuskar kwamfutar, ba ka iya ganin komai sai manhajojin da ke gabanka.  A halin yanzu kamfanin ya sake kayatar da wannan tsari na “Start Button” ya mayar da shi a bangaren hagu, inda yake a baya.  Ka ga wannan siffar “Windows 7” ce.
Akwai kuma abin da ake kira: “Windows Tiles”, wanda tsari ne da ke jera abubuwan mu’amala tsibi-tsibi a fuskar kwamfuta, ka gansu rau-rau-rau (gwanin ban sha’awa), wannan kuma siffar “Windows 8” ce.  Shi ma wannan tsari sun dada kayatar da shi a “Windows 10.”
Abu na uku, akwai masarrafar lilo (Browser) na kamfanin Microsoft mai suna: “Internet Edplorer,” wacce an dade ana korafi a kanta.  Saboda da dadewa an gano cewa galibin kwayoyin cutar kwamfuta (Computer birus) da ke addabar kwamfutocin mutane masu amfani da manhajar Windows, suna samun kafar shigowa ne ta hanyar wannan manhaja ta “Internet Edplorer.”  A halin yanzu ya bayyana cewa kamfanin Microsoft ya daina amfani da wannan manhaja ta “Internet Edplorer,” domin ya cire ta daga “Windows 10.”  Ya gina wata sabuwar manhaja mai suna: “Windows Edge” da a halin yanzu, iya gwajin da aka yi tsakanin sauran manhajojin lilo a Intanet da ke kasuwa – irin su “Mozilla Firefod” da “Google Chrome” – ya bayyana cewa manhajar “Windows Edge” da kamfanin Microsoft ke fitarwa a “Windows 10” ta fi sauran sauri da kayatarwa.  Ka ga wannan ci gaba ne ga kamfanin Microsoft ta wannan bangare.
Abu na hudu, kamfanin Microsoft ya samar da tsarin neman bayanai a kwamfuta da Intanet ta amfani da murya, a “Windows 10,” wato: “boice Search.”  A al’adance kamar yadda yake a zamanin baya, babu yadda za a yi ka baiwa kwamfuta umarni ta murya kawai har ta nemo maka bayanai.  Amma a halin yanzu akwai wata masarrafa mai suna: “Cortana,” wacce Microsoft ya fara samarwa a wata wayarsa ta salula mai suna: “Lumia 930.”  “Cortana” masarrafa ce da kamfanin ya samar a wayar salula (wacce idan ka farkar da ita, duk abin da kake yi ko duk wuraren da ka saba zuwa, ko da kasuwanni ne, za ta rika lura dasu, kuma tana taskance bayanai kan abin da ka saba yi a wajen ko taswirar wurin ma gaba daya.  Kuma a duk sadda lokacin zuwanka wannan wuri ya yi, sai ta tunantar da kai ta hanyar murya.  Sanan kana iya ba ta umarni ta tunatar da kai yin wasu abubuwa ko ta nemo maka bayanai kai tsaye daga Intanet ko cikin wayar).  A halin yanzu kamfanin Microsoft ya samar da wannan manhaja mai suna: “Cortana” don sawwake neman bayanai ta hanyar murya a cikin “Windows 10.”
Bayan wannan, akwai abin da ake kira: “Facial Recognition” (wanda tsari ne da ke iya sheda mutum ta hanyar fuskarsa nan take).  Ma’ana, za ka iya zama a gaban kwamfutarka bayan ka gama kunna ta, ka yi amfani da na’urar daukar hoto (Webcam) da ke kwamfutar a karon farko don sheda fuskarka.  Daga nan, a duk sadda kwamfutar ke kulle, da zarar ka kalli wannan na’urar daukar hoto na kwamfutar, sai babbar manhajar ta bude maka kwamfutar nan take.  Wanda a baya babu irin wannan tsari.
Ba wannan kadai ba har wa yau, akwai wani tsari da kamfanin ya kira da suna: “Windows Continuum.”  Kafin bayani kan wannan tsari, daga cikin abubuwan da suka kashe wa kamfanin Microsoft kasuwa musamman bayan bayyanar  “Windows 8,” bayan dalilan da na bayyana a baya, (shi ne raja’a da mutane suka yi wajen mu’amala da wayoyin salula da na’ururoin sarrafa bayanai).  Idan ka lura yanzu za ka ga adadin masu amfani da kwamfutoci a duniya ya ragu.  Me ya sa?  Hakan ya faru ne saboda samuwar wayoyin salula masu kayatarwa, da na’urorin mu’amala da bayanai – irin su “iPad” da “Samsung Galady Tab” misali – wadanda duk abin da za ka iya yi da kwamfuta kana iya yin sa da su.  Kuma karin amfani da suke da shi shi ne, za ka iya daukarsu a jakarka ko ka sanya su a aljihu ka yi yawonka da su.  Wannan na cikin dalilan da suka sa da dama cikin mutane suka daina sayan kwamfutoci.  Da kamfanin Microsoft ya gane wannan, sai ya tsara babbar manhajar “Windows 10” a halin yanzu, ta yadda idan kana da wayar salula ko na’urar mu’amala da bayanai irin su: iPad ko Tab da sauransu, idan ka saukar da babbar manhajar a ciki, to, yadda za ka iya amfani da “Windows 10” a kan kwamfuta haka za ka iya amfani da “Windows 10” a cikin wayar salula.  (An samar da dukkan tsare-tsaren biyu cikin babbar manhajar)…
Zan ci gaba mako mai zuwa in Allah Ya so.