Wasu karin shugabannin ’yan bindiga da suka addabi yankunan Jihar Katsina, sun tuba tare da mika makamansu ga jami’an tsaro.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Sanusi Buba ne ya bayyana hakan, a ranar Alhamis yayin da ya gana da manema labarai a jihar.
- Zaftare albashi: Kungiyar kwadago a Kano ta janye yunkurin shiga yajin aiki
- Shin DSS ce ta azabtar da direban Buhari har ya mutu?
- An nada dan ‘Shugaban Kasar Nijar’ Ministan Mai
- Ramadan: Za mu kwace lasisin duk wanda ya kara farashi —BUA
“Babu wanda muke roko ya mika wuya. Rundunar ’Yan Sanda da sauran jami’an tsaro ba za mu kyale duk wanda yaki tuba daga addabar mutane ba.
“Muna tabbatar wa da jama’a cewar ayyukan ’yan bindiga sun kusa zama tarihi a jihar nan, saboda jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu kan lamarin,” a cewarsa.
SP Buba, ya ce yana da yakinin cewa yadda shugabannin ’yan bindiga ke mika wuya, zai taimaka gaya wajen janyo hankali wasu ’yan bindigar da ajiye makamansu.
Ya ce makaman da aka sallama sun suka hada da manyan bindigogi biyu, bindiga kirar AK-49 guda daya, Ak-47 guda 23, harsashin GPMG guda 109 da kuma shanun sata guda 45.