✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin PDP zasu tattauna a yau

Shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP zasu tattauna a yau a sakatariyar jam’iyyar ta kasa a Abuja. Sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar Kola Ologbondiyan…

Shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP zasu tattauna a yau a sakatariyar jam’iyyar ta kasa a Abuja.

Sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar Kola Ologbondiyan  ne ya bayyana hakan jiya a Abuja.

Rahotanni na bayyana cewa, tattaunawar da jam’iyyar zata yi nada alaka ne, da shirin zaben Gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi da za a yi, da kuma batun shigar da karar dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Atiku Abubakar.