A ranar 17 ga Disamba 2022 ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya cika shekara 80, inda ake ganin sa a cikin mutanen da suka fi tsufa a lokacin da suke mulki.
Kawo yanzu Buhari, wanda ya hau mulki a 2015 yana da shekara 73, shi ne mutum da ya fi tsufa a kan kujerar shugabancin Najeriya.
- Tsohon Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Mahdi, Ya Rasu
- Kwamandojin Boko Haram 4 Sun Mika Wuya Ga Sojoji
Shin yaya abin yake a duniya? Albarkacin haka ne Aminiya ta kawo muku jerin shugabannin kasashen duniya biyar da suka fi tsufa a kan mulki, cikin kimanin shekara 100 da suka gabata.
1- Hastings Banda – 96
Shi ne Shugaban Kasar Malawi na farko wanda ya sauka a mulki yana da shekara 96.
Ana hasashen an haife shi 1898, inda a mulki kasar a lokuta daban-daban na tsaon 27. Ya sauka da mulki a 1994 yana da shekara 96 kafin rasuwarsa a 1997.
2- Robert Mogabe – 93
Mogabe (1924-2018) shi ne tsohon shugaban kasar Zimbabe wanda ya sauka a 2017 yana shekara 93 da wata tara, kafin rasuwarsa a shekarar 2019.
Shine shugaba mafi dadewa a tarihin Zimbabwe kuma saukarsa na cike da rudani. Rahotanni na nuna cewa sojoji sun yi masa juyin mulki, amma Kotun Kolin Kasar ta ce ya yi murabus ne don kansa.
3- Beji Caid Essebsi – 92
Shugaba Beji Caid Essebsi (1926 – 2019) na kasar Tunisiya daga 2014 zuwa rasuwarsa a kan mulki a 2019 yana da shekara 92 da wata tara.
Essebsi wanda a 2011 ya yi murabus daga matsayin Fira Minista, shi ne ya zama shugaban kasar na farko bayan Guguwar Sauyin Kasashen Laraba, bayan an gudanar da zabe.
4 – Shimon Peres – 90
Tsohon Shugaban Kasar Isra’ila na tara (2007 zuwa 2014) Shimon Peres ya sauka daga mulki yana da shekara 90 da wata 11.
Shimon Peres (1923-2016) wanda sau biyu yana zaman Fira Minista kuma ministan harkokin waje dau uku, ya sauka daga mulki ne a lokacin da shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya.
5- Joaquin Balaguer – 89
A karo biyu a lokuta daban daban (1960-1962 da kuma 1986-1996) tsohon Shugaban Kasar Jamhuriyar Dominican, Joaquin Balaguer, mulki ksaar.
Joaquin Balaguer (1907-2002) ya sauka daga mulkin sana karshe ne a 1996 yana da shekara 89 da wata 11.