Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya jaddada cewa babu yadda za a yi a kawo karsehn cin hanci a tsakanin ma’aiktan gwamnati alhali masu rike da madafun iko da dama sun ginu a kai.
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da gidan Talabijin din Trust ta shirin Siyasa cikin harshen turanci mai taken Daily Politics.
- Chelsea ta sallami kocinta, Thomas Tuchel
- An tsare mai shiga tsakani a sako fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna
Ya kara da cewa Najeriya na bukatar gwamnatin da za ta kyautata wa ma’aikata domin karfafa musu guiwar gudanar da ingantaccen aiki.
“Kana bukatar shugaban kasa da gwamna da zai fahimci cewa kashi 90 na aikin da yake takama da shi ma‘aikatan ne ke yin sa.
“Don haka kyautatawar ce za ta sanya ya yi aikin da ake bukata, har a samu nasarar fatattakar cin hanci da rashawa.
“Amma ba zai yiwu don ka biya ma’aikaci dubu 50 a wata ba, ka yi tunanin kudin da ko na motar zuwa aikin bai kai ba, zai ishe shi gudanar da rayuwa.
“Wannan ba daidai ba ne, amma ’yan siyasa suna kwashe miliyoyin kudaden al’umama.
“Me zai sanya ’yan siyasa da alakali da ministoci da gwamnoni su dinga dibar miliyoyin kudade su kadai bayan ga wadanda suke aikin da gwamnatin ke tunkaho da shi”, in ji Dokta Hakeem Baba-Ahmed.