Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume ya ce ’yan Arewa da ke shirin neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 su jira sai Shugaba Tinubu ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu a 2031.
Akume wanda ɗan yankin Arewa ne ya yi wannan kira ne musamman ga kisoshin siyasar yankin daga Jam’iyyar APC mulki da kuma jam’iyyun adawa.
“Tunda Tinubu ɗan yankin Kudu ne ya kamata a bar shi ya ci gaba da mulki wa’adi na biyu a 2027, masu son kujerar daga yankin Arewa su haƙura,” in ji tsohon gwamnan jihar Binuwan.
Akume, ya buƙaci babban abokin hamayyan Tinubu a zaɓen 2023 daga jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ke shirin sake neman kujerar da ya hakura, yana mai cewa idan Atiku na da rabo zai iya zama shugaban ƙasa yana ɗan shekara 90.
- Yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga ta faranta wa mazauna Birnin Gwari
- ’Yan bindiga sun sace amarya da ƙwayenta 4 a Sakkwato
“Idan Allah Ya nufi Atiku Abubakar da zama shugaban ƙasa zai zama ko da yana ɗan shekara 90 ne, amma a halin yanzu shi da sauran ’yan Arewa da ke son kujerar su haƙura Tinubu sai bayan Tinubu ya yi wa’adi na biyu daga 2027,” in ji sakataren gwamnatin.
A yayin hirar da kafar talabijin ta TVC ta yi da shi, Akume ya bayyana cewa yanzu lokacin yankin Kudu ne na ci gaba da mulkin Nijeriya na tsawon shekara takwas.
A cewar tsohon gwamnan jihar Binuwan, har yanzu Shugaba Tinubu na da farin jini a wurin ’yan Nijeriya, duk kuwa da ƙudurin sabuwar dokar haraji da ma sauran tsare-tsaren gwamnatinsa ta ɓullo da su a tsawon watanni 17 dasuka gabata.
A cewarsa, dokar harajin abu ne mai kyau da zai amfani Nijeriya idan aka aiwatar da ita.
“Dokar ta yi kyakkyawan Tanadi ga Najeriya da ’yan ƙasar, a shirin Shugaba Bola Tinubu na inganta tattalin arziƙin ƙasar kamar yadda ya yi ta hanyar cire tallafin man fetur da haɗe harkar hadahadar canjin kuɗaɗe.
“Barna abu ne mai sauƙi, amma sake gina abin da aka lalata na da wuya. Tinubu yana ƙoƙarin gyara ɓarnarnda gwamnatocin baya suka yi ne, kuma nan gaba za a fara cin moriyar waɗannan tsare-tsaren da ya ɓullo da su,” in ji sakataren gwamnatin.
Don haka ya bukaci ’yan ƙasar da su ba da goyon bayan domin kammala aiki a kanta.