Babban Hafsan ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali, ya bukaci kotu ta soke hukuncin daure shi a gidan yari.
Shugaban ’yan sandan na neman haka ne a gaban Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja bayan wata kotu ta sa a daure shi na wata uku a gidan yari kan raina umarninta na dawo da Patrick C. Okoli bakin aikinsa na dan sanda da aka sallame shi ba bisa ka’ida ba.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya ce, “Tun kafin a nada Alkali a matsayin Shugaban ’Yan Sanda, magabacinsa ya dauki matakan doka don aiwatar da umarnin dawo da Patrick C. Okoli, wanda ya shigar da kara, bakin aikinsa.”
Don haka Shugaban ’Yan Sandan ya bukaci kotu ta soke hukuncin, domin ba shi ne ke kan kujerar ba a lokacin da aka ba da umarnin da kotun baya ta ce ya saba.
Bukatar da Sufeto-Janar din ya shigar a ranar Alhamis ta bayyana cewa tun kafin umarnin kotun da ka bayar a watan Nuwamban 2018 da Janairu 2019, magabacinsa ya aike wa Hukumar Kula da Harkokin Aikin Dan Sanda (PSC), takardar neman ta bai wa Okoli takardar dawo da shi bakin aiki da kuma kara masa girma zuwa matakin da ya dace.
Adejobi ya ce, don haka, “Babu bukatar zaman kotun.
“Shugaban rundunar na ba wa ’yan Najeriya tabbacinsa na bin doka da oda, don haka babu yadda za a yi saba umarnin kotu.”