Shugaban Kasar Tanzania John Pombe Magufuli ya riga mu gidan gaskiya.
Mataimakiyarsa, Samia Suluhu ce ta sanar da rasuwar Mista Magufuli a kafar yada labaran kasar.
- Ahmad Lawan ya roki Saudiyya ta sako ’yan Najeriya 10,000 da ta tsare
- ’Yan bindiga na samun taimako daga kasashen waje —NSCDC
Magufuli ya rasu a ranar Laraba a wani asibiti Dar es Salaam, babban birnin kasar inda ya yi jinya ta ciwon zuciya.
Saluhu ta ce a ranar 14 ga watan Maris ne jikin shugaban ya yi tsanani inda kuma aka kwantar da shi a asibiti.
Rahotanni sun bayyana cewa ya shafe fiye da shekara 10 yana fama da larurar.
Magufuli ya bar duniya yana da shekaru 61.