Hukumomi a Sri Lanka sun tseratar da shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa daga fushin masu zanga-zanga a wannan Asabar.
Dubban masu zanga-zangar sun bukaci shugaban Sri Lankar da ya yi murabus bisa zarginsa da almubazzurancin da ya jefa kasar mai mutane miliyan 22 cikin matsanancin talauci.
- Ya nemi agolansa ya biya diyyar rainonsa da ya yi
- Jami’an tsaro sun yi bakin kokarinsu wajen kare gidan yarin Kuje —Dingyadi
Masu zanga-zanga a Sri lanka sun mamaye gidan shugaban kasar a Colombo, inda suke bukatar ya sauka daga shugabancin kasar.
Dandazon masu zanga-zangar da ke daga tutoci sun yi dirar mikiya zuwa gidan shugaban kasar, tare da wuce shingen jami’an tsaro, kan yadda shugaban Gotabaya Rajapaksa ke tafiyar da al’amura a kasar da ke cikin matsin tattalin arziki na shekaru goma.
Hotuna a kafofin sada zumunta sun nuna masu zanga-zangar sun kutsa har cikin dakin kwanan shugaban kasar inda suka rika daukar hotuna a kan gadonsa da zama kan kujeru.
Da dama daga cikinsu kuma sun afka cikin wurin wanka na alfarma wato swimming pool inda suka yi ta wanka a ciki.
An shafe watanni a kasar dai ana zanga-zanga inda za iya cewa kudaden waje sun kare a kasar wanda hakan ya sa ba a iya sawo kayayyakin amfanin yau da kullum kamar su fetur da magani da abinci.
Makarantu ma sun shafe kusan makonni uku a rufe saboda wahalar man fetur.
Rahotannin sun bayyana cewa shugaban na Sri Lanka ya amince ya yi murabus bayan bukatar hakan da ’yan majalisar kasar da jam’iyyarsa suka nuna.
Dan siyasar ya ce zai dauki matakin domin wanzar da hadin kai a tsakanin ’yan kasar.