Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a Landan.
A halin yanzu shugaba Buhari yana ziyara a Birtaniya ne domin ganin likitansa.
- An kama direban Adaidaita Sahu kan zargin sace wa fasinja wayar salula
- An sallamo Sarki Salman daga asibiti
Buhari ya kuma amince Mai Mala Buni ya ci gaba da jagorancin APC a matsayinsa na shugaban kwamitin riko na jam’iyyar, kamar yadda Hon Faruk Adamu Aliyu jigo a jam’iyyar APC ya shaida wa BBC.
Ya ce Buhari ya amince Mai Mala Buni ya ci gaba da aikin jagorancin babban taron jam’iyyar da ake shirin gudanarwa a ranar 26 ga watan Janairu, duk da wani umarnin kotu da ya ce a dakatar da taron.
Shugabancin APC ya shiga rudani ne a karshen watan Fabarairu tun bayan da Gwamnan Neja Abubaukar Sani Bello ya ayyana kansa a matsayinsa mai jagorancin kwamitin.
Daga baya kuma wata wasika ta bulla cewa Mai Mala ne ya ba shi riko saboda ya yi tafiya kasar waje don a duba lafiyarsa, bayan da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ce sam ba ta san wannan zancen ba.
Rikicin shugabanci a APC ya kara kamari ne tun bayan da wasu gwamnoni, ciki har da Nasir El-Rufai na Kaduna, suka ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin a sauke Mai Mala Buni, wanda ya fara jagoranci tun watan Yuni na 2020.